Matashin saurayi Musulmi ya kashe kanshi akan an hana shi buga Game

0
475

Abin takaici ne labarin wani matashin saurayi da ya kashe kanshi akan wani abu dan kankani. Matashin saurayin mai shekaru 20 a duniya da ya fito daga Lahore Saddar Bazaar, ya rataye kanshi a jikin fanka.

Dalilin da ya sanya shi yin hakan kuwa abu ne mai sauki. Ya kashe kanshi dinne bayan mahaifinsa ya hana shi buga GAME.

A yadda rahoto ya nuna yaron da ake yi masa inkiya da Jonty, ya samu sabani da mahaifinsa akan buga Game din ta yanar gizo, cewar Express News.

Washe gari da safe iyayenshi sun iske gawarshi rataye a jikin fanka a cikin dakin shi.

Matashin saurayin yana karatu a Kwaleji ne. Yana matukar son buga wasan Game din. Sannan kuma yana aikin gyaran gashi a wani shago domin taimakawa iyayenshi.

Idan ya gama aiki yana zuwa ya buga wannan wasa a wayar shi har zuwa tsakiyar dare. Wannan wasa na wayar salula yana kara yin suna a wajen matasa.

Sai dai kuma yawan buga wasan na iya sanyawa mutum ya samu matsalar kwakwalwa. Wannan ita ce matsalar da matashin saurayin ya samu.

Bayan shafe lokaci yana buga wannan wasa matashin saurayin ya fara fita daga hayyacinsa, inda ya fara nuna alamu na tabin hankali. Wannan labari dai ya zo ne a wannan lokaci na Coronavirus da yawancin kasashe suka hana zirga-zirga.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here