Matashin Saurayi da ya Musulunta a watan Ramadana ya bayyana irin shauki da farin cikin da ya tsinci kanshi a ciki

2
6499

Wani saurayi mai suna Anthony Michael ya bayyana yadda ya musulunta a cikin watan Ramadana mai alfarma.

Bayan wallafa hotuna masu kayatarwa da ya dauka a lokacin da ya karbi kalmar shahada, ya ce yayi farin ciki sosai da irin goyon bayan da ya samu a shafin Twitter tun lokacin da ya bayyana musuluntar shi.

Michael ya ce “Musulunci addini ne na kaunar juna, kyautatawa da kuma zaman lafiya,” ya ce ‘yan kwanakin nan ya same su cikin jin dadi sosai.

Anthony Michael da abokanan shi Musulmai bayan ya karbi kalmar shahada (Hoto: @anthrauhl)

Ya ce sakonnin da ya karba daga wajen ‘yan uwa maza da mata Musulmai sune suka kara masa jin dadi da karfin guiwar shiga addinin da karfin shi.

Ga dai abinda ya rubuta a shafinsa na Twitter.

“A karshe dai na Musulunta a cikin watan Ramadana mai alfarma.”

Anthony Michael da abokanan shi Musulmai bayan ya karbi kalmar shahada (Hoto: @anthrauhl)

“Kalmar shahada dana karba jiya ita ce abu mafi kyau da ya taba faruwa dani a rayuwata, kuma ina matukar godiya da irin goyon bayan dana samu daga wajen abokanai na. Kasancewar na karbi sakonni masu yawan gaske daga wajen ‘yan uwa Musulmi maza da mata, hakan ya sanya ni cikin farin ciki marar misaltuwa.”

Anthony Michael da abokanan shi Musulmai bayan ya karbi kalmar shahada (Hoto: @anthrauhl)

Anthony ya kara da cewa:

“Nayi farin ciki kwarai da gaske da irin soyayyar dana samu a wannan manhaja. Watanni kadan da suka wuce na kasance cikin farin ciki. Musulunci ya sanya ina ji na zama mutumin kirki. Musulunci addini ne na soyayya, kyautatawa da kuma zaman lafiya.

Anthony Michael da abokanan shi Musulmai bayan ya karbi kalmar shahada (Hoto: @anthrauhl)

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here