Matashi ya yiwa matar yayanshi fyade ya kasheta a jihar Zamfara

0
618

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, da yake gabatar da mai laifin a ranar Litinin, ya ce tuni saurayin mai suna Bala ya amsa laifinsa.

Ya ce mai laifin dan asalin kauyen Damaga ne dake cikin karamar hukumar Maradun.

Ya ce:

“A ranar Litinin 15 ga watan Yuni da misalin karfe 4:30, ofishin ‘yan sanda na Tudun Wada sun samu kiran waya daga unguwar Damba dake Gusau, cewar mai laifin ya kashe matar yayanshi.

“Cikin gaggawa ‘yan sanda suka garzaya wurin da lamarin ya faru, suka tarar da matar mai suna Hauwa’u Iliyasu a cikin jini, inda ya sassarata da adda.

“An garzaya da ita zuwa asibitin kwararru na Yariman Bakura dake Gusau, inda likitoci suka tabbatar da cewa ta mutu.”

Kakakin rundunar ya kara da sun tuntubi mijin matar a waya mai suna Kabiru Bala.

“Baya jihar ma baki daya, amma ya tabbatarwa da ‘yan sanda cewa dama ya taba yi mata barazanar kisa,” ya ce.

Shehu ya ce yanzu suna jiran dawowar mijin marigayiyar, wanda zai bayar da bayani da za su gabatarwa da kotu a lokacin da suka kai mai laifin a yanke masa hukunci.

Hauwa’u dai ta mutu ta bar ‘ya’ya guda biyu, ciki hadda jariri mai wata tara a duniya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here