Matasa sun kone wani mahaukaci da ya tarar da wasu yara guda biyar suna wasa ya hau su da sara da adda sai da yaga bayan su

0
1220

A ranar Asabar din nan da ta gabata ne wasu matasa suka kone wani mahaukaci mai suna Oladele Adeola, mai shekaru 35, bayan ya kashe ‘yan uwansa guda biyar a lokaci daya, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Lamarin ya faru a kauyen Ojaodan dake yankin jihar Legas da misalin karfe 9:30 na safe.

An ruwaito cewa Adeola yayi amfani da adda ne wajen daddatsa yaran da suke da tsakanin shekara biyu zuwa biyar. An ruwaito cewa yaran ‘ya’yan wani mutumi ne mai suna Olaegbe Adeola.

Yaran masu suna Bolu, Johnson, Tosin, Joel masu shekara biyar-biyar sai kuma Sesan mai shekara biyu.

An ruwaito cewa yaran suna wasa ne a lokacin da mahaukacin ya isa wajen da adda a hannunshi ya fara saransu.

Kafin mutanen kauyen su ankara tuni har yaran su mutu a take a wajen.

An ruwaitoc cewa ganin gawarwakin yaran a kasa ya tunzura matasa suka kama mahaukacin suka sanya masa wuta.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar The Nation.

Ya kara da cewa iyalan yaran sun tilasta ‘yan sanda suka basu gawarwakin yaran suka binne duk da shawarar da ‘yan sandan suka bayar akan aje asibiti a gabatar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here