Matasa sun kashe wani mutumi akan ya saci kaza zai ciyar da ‘ya’yanshi guda 7 da yunwa ta dame su

0
1164

Matasa sun kashe wani mutumi mai ‘ya’ya guda bakwai a kauyen Kamurojjo-Muro, dake Serere, yankin Teso cikin kasar Uganda.

Mutumin da aka bayyana sunanshi da Emuron an zarge shi da satar kaza a gidan makocinsa, a ranar Litinin da rana, inda mutanen gidan suka yi masa rubdugu suka kashe shi.

A yadda Eastern News Network ta ruwaito, wani wanda lamarin ya faru akan idonshi ya bayyana cewa ya jiyo lokacin da Emuron yake bayyana musu cewa “ya’yanshi sun shafe kwanaki ba tare da abinci ba.”

Shaidar mai suna Paul Edigu, ya ce matasan ba su bawa mutumin damar yin magana ba suka hau shi da duka.

“Duk da wannan abu da ya faru dai, wasu daga cikin mutanen yankin sun bayyana cewa wannan doka ta hana zirga-zirga da aka sanyawa mutane ita ce ta sanya Emuron zuwa ya saci wannan kaza don ya ciyar da iyalin shi,” Edigu ya sanar da ENN.

Bayan an barshi rai a hannun Allah, wasu da suke da dan tausayi a cikinsu sun dauke shi zuwa asibiti, amma suna zuwa ya mutu, inda aka ajiye gawarshi a kasan bishiyar mangwaro a cikin asibitin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here