Matar aure tayi bayanin yadda ta koma kwanciya da mutumin da suke haya a gidansa domin ta samu kudin da za ta ciyar da mijinta da ‘ya’yansu

4
572

Wata mata ta nemi shawarar fitacciyar matar nan mai bada shawara akan zamantakewar aure, Vivian Valerian Raphaels, inda ta bayyana abinda take yi take ciyar da iyalinta a wannan lokacin.

Kamar yadda matar ta bayyana, tana kwanciya da mutumin da suke yin haya a gidansa domin ta ciyar da mijinta da kuma ‘ya’yansu. Matar ta ce yanzu duk kunya tabi ta isheta tana neman shawara.

“Dan Allah ki boye sunana, nayi aure shekaru 10 da suka wuce da yara guda uku yanzu. Mijina shekarunsa 44, ni kuma shekaruna 32 yanzu. Ina rokonku kada kuga laifina sosai. Ina neman shawara ne kawai domin na taimakawa kaina, saboda yanzu haka na fara tsanar kaina.

“Mijina ya rasa aikinsa shekaru 2 da suka wuce, tun daga wannan lokacin ni nake ciyar da duka gidan da albashina. Nayi wani abu da ban so na kara yi a wannan lokaci na Corona. Bani da wani kudi kuma bamu da sauran abinci, sannan babu wanda zan iya tambaya, hatta ruwan sha sai na burtsatse muka fara sha.

“Ni da iyalina mun kwana biyu cikin yunwa, sai naje na tambayi mai gidan da muke haya a wajensa kudi. Duka makwabtanmu naje wajensu babu wanda ya taimaka mini. Ina yiwa mijina karya akan zanje wajen dan uwana ko zan samu kudi a wajensa, matar mai gidan da muke haya a wajensa da ‘ya’yan duka suna kasar waje, sai shi daya a gidan.

“Gida biyu ne kawai ya raba mu da nashi. Da naje gidan shi sai ya kara dauko mini maganar iskanci, nace masa ba zan iya ba, yayi alkawarin bani dubu ashirin kyauta da kuma kayan abinci. Na san abinda nayi ba daidai bane, domin kuwa duk naji na tsani kaina. Amma ba zan iya cigaba da kallon ‘ya’yana suna kuka ba, haka ya saka na amince.

‘Tun daga wannan lokacin nake rokon Allah ya yafe mini, saboda inda ace sun biya mu albashi a wajen da nake aiki da duka haka bata faru ba.

“Bayan kwana uku mutanen gidanmu suka gana da shi, haka masu yankan wuta suka zo suka yanke, idan kunga yadda ya ciwa mijina mutunci akan ya bayar da shawara, saboda ya riga ya san halin da muke ciki, kunya ta saka na rufe fuskata. Nayi dana sanin abinda nayi. Mijina baya hawa kafafen sada zumunta, dan Allah ki taimaka ki sanya ko zan samu wasu su bani shawara.” inji ta.

4 COMMENTS

  1. Subhanalillahi laifi dai anyi amma cikin kuskure sai dai tanima Allah yayafe mata , shawara kuma kamata yayi sunima taimakon iyayenta ko iyayen mijinta ko yanuwanta ko yanuwan mijinta , in hakan bai yiwu ba shi mijin yakamata tabashi shawaran ko aikin kodigo ne yaje yayi dan rufin asirin su , amma ba afada sabon Allah ba kokuma kunima taimako dan na Allah basukarewa

  2. Allah ya yafe mata yakuma basu halin da zasu iya rike Kansu batare da fadawa irin wannan halakaba kuma shawara shine bawanda tadace matannan tanama sai danginsu daga farko inhar makwabta sungazayin hakan nikuma taimakon dazanyi mata intana bukata shine sai munyi waya sai inji yadda zaayi intaimaka mata da gudumawata 08149127498

  3. Laifide anriga anyi Tacigaba da Tuba Allahu ghafururrahim kuma Allah Yanason masu Tuba Amma yakasance Taubatan nasuha

    Allah Ya kawomusu mafita
    Allah Ya karemu bakidaya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here