Matar aure ta tsinkewa mijinta gaba bayan ta kama shi yana lalata da wata

0
1058

Wata mata mai shekaru 35, mai suna Mrs Omolara Seriki, ta lalata gaban mijinta mai suna Raheem, mai shekaru 52 a duniya, bayan ta kama shi yana lalata da wata mata a yankin Iragbiji dake jihar Osun.

Da yake bayyana haka ga manema labarai, kakakin hukumar Civil Defence na jihar, Daniel Adigun, ya ce ma’auratan sun samu matsala a auren nasu wanda suka shafe shekaru 6 suna tare, hakan ya sanya su suka raba gida.

Sai dai kuma a ranar Talata 23 ga watan Yuni, matar taje gidan da mijin nata yake zaune, inda ta same shi da wata a gidan. Rikici ya balle tsakaninsu, a garin fadan da suke ta kama gaban shi ta tsinke.

A cewar kakakin hukumar NSCDC, Mr Adigun, “Matar ta kai wa mutumin abinci ne da misalin karfe 10 na dare, sai ta kasa tafiya gida saboda ruwan sama da ya barke.

“Ba a jima ba sai ga matar shi ta isa gidan, ai kuwa sai rikici ya barke wanda yayi sanadiyyar da tayi wannan aika-aika.

“Bayan ta lalata masa gaban ya sume a wajen bai dawo hayyacinsa ba sai a asibiti inda aka dinke masa gaban nasa.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here