Matar aure ta rasa ‘ya’yanta guda 3 bayan ta yiwa kawarta dariya akan bata haihuwa

0
534

Wata mata da ta rasa ‘ya’yanta guda uku bayan ta yiwa kawarta dariya akan bata haihuwa ta koma tana neman gafararta.

Wata ‘yar Najeriya dake zaune a kasar Canada mai suna Obianuju Pepertual Kanu, ita ce ta wallafa haka a shafinta, inda ta bayyana yadda daya daga cikin kawayenta da take yawan tsokanarta akan bata haihuwa ta rasa ‘ya’yan nata guda uku.

A cewarta kawarta mai suna Nneka, ta dauki kayan sawarta ba tare da ta tambayeta ba, lokacin da ta bukaci ta dawo mata da kayanta, Nneka ta fara zaginta tana tsokanarta akan bata haihuwa.

Ba a iya zagi da tsokana lamarin ya tsaya ba, ta sanya ‘ya’yanta su jefe ta daga cikin gidansu.

Matar wacce ta nuna bacin ranta akan abinda kawartan tayi mata, ta ce lamarin ya faru a shekarar 2006, sai a wannan shekarar ta 2020 kawartan ta kirata ta roketa akan ta yafe mata.

Ta ce matar ta ce mata ta je wajen Fasto bayan ‘ya’yanta guda uku sun mutu, kuma Faston ya gaya mata cewa akwai matar da ta yiwa dariya akan bata haihuwa, saboda haka dole sai ta nemi gafararta kafin komai nata ya koma daidai.

Obianuju ta ce ta yafewa Nneka da zuciya daya, sannan ta shawarci mutane da kada su yiwa wani dariya akan kowanne abu na rayuwa, “ku yi musu addu’a mai makon yi musu dariya” ta ce.

It's 1am Canadian time today I received a call from Nneka . She asked how I am doing and if I have kids and I said of…

Posted by Obianuju Perpetual Kanu on Thursday, June 18, 2020

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here