Matar aure na neman kashe kanta bayan bidiyon da tayi na batsa da wani saurayi ya bazu a shafukan sadarwa

0
6100

Babu dadin ji kwata-kwata yadda wasu mutanen ke ganin cewa kashe kansu shine mafita a lokacin da suke cikin tashin hankali.

Wata mata tayi yunkurin kashe kanta bayan bidiyon da tayi na batsa da wani ya bazu a kauyensu, wanda ya jawo mata abin magana sosai.

A rahoton da Adomonline.com ta ruwaito, matar mai suna Maame Mary, an dauke ta suna fim din batsa da wani, inda daga baya kuma aka yada fim din ya bazu a kauyensu.

Bidiyon na matar auren ya jima yana yawo a cikin kauyensu, inda mutanen da suka ga bidiyon suke zuwa har cikin shagonta su ci mata mutunci.

Matar wacce abin duniya yayi mata yawa ta bayyana cewa saurayin ya yaudareta ne bayan ita ta dauke shi a matsayin amini, ta ce kawai ta tashi daga bacci ne ta iske kanta akan gadonshi.

“Ya gayyace ni cin abinci, daga baya naji duk jikina yayi nauyi. Washe gari kawai na tashi na iske kai na akan gadonshi. Daga baya na gano cewa ya dauki bidiyon lokacin da yake lalata dani ya turawa abokanan shi,” cewar ta.

Maame Mary ta ce wannan lamari ya kusa ya kawo karshen aurenta da mijinta, amma da yake mijinta mutum ne mai fahimta ya fuskanci halin da take ciki.

Ta kai karar lamarin ga ‘yan sanda, amma a cewarta ‘yan sandan kawai sun yiwa mutumin gargadi ne inda har yanzu yake gari yana yawo abin shi.

Maame Mary an ruwaito cewa tana kokarin kashe kanta saboda abin duniya da yabi yayi mata yawa, ta kuma dawo da darajar mijinta da ta danginta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here