Masha Allah: Na daina yawo tsirara saboda ni’imar addinin Musulunci – Jarumar Hollywood Sara Bokker

0
368

Idan muna magana akan matan Amurka, abu na farko da yake zuwa zuciyarmu shine, mace da take yawo tsirara, wacce take zuwa gidan rawa a koda yaushe, mace marar kamun kai. Sai dai kuma akwai wasu tsirarun mata ‘yan kasar Amurkan da sun san cewa wannan rayuwa ba ita ce rayuwar da ta dace da mata ba.

Shin wata hanya ce ya kamata mace tabi don zama cikin amince da ‘yanci? Amsar wannan tambaya na cikin labarin wata Musulma da ada tayi irin wannan rayuwa.

Sara Bokker wacce take jaruma ce a fina-finan Turawa na Hollywood, an haifeta a kasar Amurka. Ta girma kamar kowacce budurwa a kasar Amurka, ta tashi cikin birni kanta a waye.

Tayi suna matuka wajen nuna kanta da kuma irin halittar da Allah yayi mata, tana rayuwa mai tsada.

Bayan rayuwa tayi nisa sai ta fara dawowa cikin hayyacinta, inda ta gane cewa akwai abubuwa da yawa da take yi wanda bai kamata ba, daga nan sai ta fara daina shan giya ta kuma daina zuwa wajen rawa.

A karon farko ta gane cewa mutane duka daya ne a wajen Allah. Amma ta gane cewa mai imani ne kawai zai iya gane wannan hikima ta Allah.

Watarana sai ta samu Qur’ani, amma kafin wannan lokaci ita kallon da take yiwa addinin Musulunci shine kawai ana takura mata suna sanya abinda basu so, sannan maza na dukan matayensu, da kuma koyar da ta’addanci.

Bayan karanta littafi mai tsarki, ta samu kanta cikin wasi-wasin abinda take yi a baya, Qur’ani ya sanya mata wata nutsuwa, bayan ta karanta ta ga cewa shi littafine da mutum zai iya nazari a kai ba tare da ya bukaci fasto ya gaya masa abinda zai yi ba.

A hankali ta samu nutsuwa sosai da addinin Musulunci, inda a karshe ta karbi kalmar shahada ta fara rayuwarta cikin aminci.

Ta siyo doguwar riga da niqabi ta fara shiga irinta Musulmai ta fara yawo akan titin unguwarsu wanda ta saba yawo a kai lokacin da take shigar tsiraici.

A karshe taji rayuwarta tayi mata dadi sosai, bata zuwa siyan kayan kwalliya, ko kuma zuwa wajen gyaran gashi da dai sauran abubuwa da take yi a baya na almubazzaranci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here