Masha Allah: Mace Musulma ta zama gwamna ta farko a kasar Canada

0
1258

Firaministan kasar Canada Justin Trudeau, yayi sababbin nade-nade a ‘yan kwanakin da suka gabata. Wannan nade-nade da yayi abin alfahari ne ga Musulman duniya baki daya.

Salma Lakhani – ‘yar kasuwa kuma mai taimakon al’umma dake zaune a Alberta ta samu mukamin gwamna, inda ta zama Musulma ta farko da aka taba bawa wannan mukamin a tarihin kasar Canada.

A wata sanarwa da Firaministan ya fitar, ya ce: “Ms Lakhani ta jima tana taimakawa al’ummar yankinta, daga sababbin baki, matasa da kuma mata da yara.

“A matsayin gwamnar Alberta, na san za ta yiwa mutanen jiharta hidima dama kasa baki daya, sannan kuma za ta zama abin koyi ga duka al’ummar kasar nan.”

Lakhani an haifeta a kasar Uganda, sai ta koma Canada da zama, a lokacin da tsohon shugaban kasar Idi Amin ya tilasta su barin kasar.

Tana da dangantaka da kasar Indiya, ta koma Edmonton da zama a shekarar 1977 tare da mijinta da kuma ‘ya’yanta guda biyu.

Sabuwar gwamnar ta Alberta, mace ce mai son taimakon al’umma, inda take aiki tukuru wajen tallafawa al’ummar yankinta.

Salma dai za ta karbi kujerar Lois Mitchell, wanda ya rike mukamin gwamnan jihar ta Alberta a baya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here