Masha Allah: Kyakkyawar budurwa ‘yar kwallon kafa a kasar Sweden ta karbi kalmar shahada

0
581

Kyakkyawar budurwa mai shekaru 20 a duniya da take buga kwallon kafa a kungiyar kwallon kafa ta mata ta Sweden’s Uppsala, ta karbi kalmar shahada.

Budurwar wacce take mai tsaron raga, mai suna Ronja Andersson ta karbi kalmar shahada, inda kuma ta bayyanawa duniya kowa ya san da shigowar ta Musulunci.

A cewar Ronja, abokinta ne ya fara sanar da ita addinin Musulunci tun tana shekara 15 a duniya. Tun daga lokacin ta fara jin kaunar addinin a ranta. Daga nan taje kasar Turkey, inda ta ga yadda addinin Musulunci yake.

Tayi matukar mamaki da taji yadda ake kiran Sallah, inda tun daga lokacin ta fara bincike akan addinin Musulunci.

“Na gano cewa akwai abubuwa da dama da suka jawo mini hankali. Daga nan na fara zuwa wajen taron addini da kuma Masallaci,” cewar Rojna a wata hira da aka yi da ita.

A wata hira da tayi da manema labarai na kasar Sweden, Rojna ta bayyana dawowarta addinin Musulunci, inda ta ce tana alfahari da zamanta Musulma duk kuwa da karan tsanar da wasu suka sanya mata. “Suna nuna mini tsana a fili saboda na shigo addinin Musulunci.”

An bayyana cewa ta samu matsala sosai daga wajen mutane ciki kuwa hadda iyayenta a lokacin da ta yanke shawarar shigowa addinin Musulunci. Har sako aka dinga aika mata na barazana dana kyama akan shigowarta Musulunci, amma duk da haka bata razana ba.

Ta ce addinin Musulunci addini ne mai kyau, kuma tana yin iya bakin kokarinta wajen yin salloli akan lokaci sannan tana yin azumi a watan Ramadana.

Wannan jajircewa da budurwar tayi da kuma nuna rashin razana ya sanya wadanda suke yi mata barazana suka saduda, inda wani da ya aika mata da sakon barazana ya fito a gidan talabijin yana rokonta akan ta yafe masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here