Masha Allah: Dattijo dan kasar Saudiyya ya rubuce Al-Qur’ani mai girma baki daya a jikin kwai guda 6

0
2456

Wani dattijo dan kasar Saudiyya mai shekaru 70 a duniya ya rubuce AL-Qur’ani mai girma a jikin kwai guda shida, ta hanyar rubutu mai ban sha’awa. Soyayya ga Al-Qur’ani, Makkah da Madina, dabi’a ce gama gari ta Musulmai.

Musulmai da yawa suna nuna so da kaunarsu ta hanyoyi daban-daban, amma akwai ‘yan kalilan da suke wuce gona da iri, suke yin abubuwa wadanda basu kamata ba da sunan soyayya.

Wannan dai labarin wani dattijo ne dan kasar Saudiyya, wanda ya sadaukar da lokacinshi da karfinshi wajen rubuta Al-Qur’ani a jikin Kwai. Hakan zai zama ban barakwai, amma ita soyayya ba ruwanta da haka.

Dattijon yana ganin rubutu a jikin kwan ita ce hanya guda daya da zai nuna soyayyarshi. Sunan dattijon Ahmed Abdan, ya shafe rayuwarshi baki daya wajen rubuce-rubuce masu ban sha’awa na Larabci.

Abdan ba wai iya rubuta Qur’anin yayi a jikin kwan ba kawai, ya kuma haddace Qur’anin a lokacin da yake rubutun. Abdan shine mutum na farko da ya fara yin wannan abu duk kuwa da tsufan da yake da shi.

Abdan yana rubuta Qur’anin a jikin kwan a tsaye ne, idan kuwa mutum yana so ya karanta sai yayi amfani da na’urar kara gani saboda rubutun yayi kankanta da yawa da ido ba zai iya gani ba.

Mutane na ta yabawa Abdan akan wannan baiwa da Allah ya bashi. Allah ya bashi rayuwa mai tsawo mai amfani. Wani mutumi shima dan kasar Indonesia ya rubuta Al-Qur’ani baki daya a jikin itace.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here