Masha Allah: Bayan shafe shekaru 700 babu Masallaci, Musulmin dan kwallon kafa ya fara gina Masallaci a birnin Sevilla

0
3779

Tsohon dan wasan kwallon kafa, da tauraruwar shi ta haska a shekarun baya, Frederick Oumar Kanoute, ya bayyana cewa yayin da ya gama shirye-shirye tsaf, ma’aikata sun fara ginin Masallaci na farko a birnin Sevilla dake kasar Spain, bayan shafe shekaru sama da 700 babu Masallaci.

Kanoute wanda yake dan asalin kasar Mali, amma yake zaune a kasar Faransa, ya bayyana fara ginin Masallacin baya ya tara dala miliyan daya a wata gidauniya ta neman taimako wacce ya bude a shafukan sadarwa.

Da yake sanar da ginin Masallacin, fitaccen dan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Sevilla, ya aika da sakonnin godiya ga al’ummar da suka bayar da tallafi akan ginin Masallacin.

Kanoute ya ce: “Ina mika godiya ta a gareku, Allah ya bada lada ga wadanda suka tallafa ta kowacce hanya wajen hada kudin ginin Masallacin nan,” kamar dai yadda fitaccen dan wasan ya sanya a shafinsa na Twitter.

Banda ginin Masallacin, za a kuma gina cibiyar al’adu da tarihi saboda Musulman dake birnin na Sevilla.

Wannan gini da za a kasar zai zama na farko a tarihin birnin na Sevilla baki daya cikin shekaru 700.

Fitaccen dan wasan ya Musulunta tun yana dan shekara 20 a duniya, ya sanar da Aljazeera cewa ya sha bakar wahala wajen neman Masallaci a lokacin da ya koma kungiyar kwallon kafa ta Sevilla a kasar ta Spain.

“Na wahala sosai wajen neman Masallaci a lokacin dana dawo Sevilla, sai dana dinga tambayar mutane inda zan samu Masallaci nayi sallah,” a cewar Kanoute.

Dan wasan ya cigaba da cewa a birnin na Sevilla akwai Musulmai sama da 30,000, inda ya ce yawancinsu bakin haure ne da suka fito daga kasashen Afrika irinsu Mali, Senegal, Morocco da Algeria, sai kuma mutane kalilan ‘yan asalin kasar ta Spain da suka Musulunta.

A baya dai Kanoute ya taba siyawa Musulmai wurin sallah a kasar a lokacin da suke samun barazana ta rashin wurin ibada sanadiyyar kudin hayar da suke na wajen ibadar da ya kare.

Dalilin haka ne fitaccen dan wasan ya kafa wannan gidauniya ta neman tallafi don ginawa Musulman na birnin Sevilla Masallacin yin ibada na har abada.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here