Masha Allah: Baturiya da ta karbi Musulunci kuma ta Musuluntar da Turawa 1000 a kasar Belgium

0
1989

Shin kun taba jin kalmar Kiristoci da ake kiran su da suna ‘Mishan’? Na san da yawa mun sha jin wannan kalmar, ina tsammani.

Mishan wata kungiya ce ta kwararrun masana ta Kiristoci da ake tura su kasashen da basu da arziki suke mayar da mutanen garuruwa zuwa addinin Kiristanci, ta hanyar basu kudi ko kuma dai wata hanya daban.

Ta wannan hanyar ne addinin Kiristanci yayi karfi sosai a yawancin kasashen yankin Asiya da kuma kasashen Amurka.

Sai kuma addinin Musulunci a yanzu da yake addini na biyu da yafi yawan al’umma a duniya, kuma addinin da yafi yaduwa a duniya a halin yanzu. Shin Musulunci yana da irin wannan kungiyoyi na Mishan a duniya kuwa? Amsar ita ce a’a.

To daga yaya Musulunci yake bunkasa a duniya a wannan lokacin? Amsar wannan tambayar na cikin wannan labari da zamu kawo muku a kasa.

Wata ‘yar uwa daga kasar Belgium ba wai ta Musulunta bane kawai a lokacin da take budurwa, ta kuma taimakawa kimanin mutane 1000 sun gane addinin Musulunci kuma sun Musulunta.

Veronique Cools | Photo Source: Facebook

Tayi duka wannan aiki ne ba tare da taimakon kowa ba, to ma mai yasa za ta nemi taimako, idan har za tayi mutane wa’azi akan su dawo addinin Allah.

Sunanta Veronique Cools ta Musulunta a lokacin da take ‘yar shekara 13 a duniya. Yanzu shekarunta 31 a duniya, a shekarun baya ta taimakawa mutane da dama wajen karbar addinin Musulunci.

Kamar yanda addinin Musulunci bashi da wani karfi a kasar Belgium, Cools taji addinin ya kwanta mata matuka. Kawayenta ne suka sanya mata son addinin a lokacin da take makaranta.

Veronique taji kaunar addinin sosai a ranta, hakan ya sanya ta fara bincike a kanshi. Ta dinga neman taimako a wajen Malaman addinin Musulunci na kasar Turkiyya dake kasar Belgium.

Cikin lokacin kankani Veronique ta yarda cewa addinin Musulunci shine addini na gaskiya, kuma za ta iya sanin Allah ta wannan addini. Sai kawai ta karbi addinin Musulunci.

Amma a farko abin babu sauki a gareta, saboda mutanen kasar Belgium suna yiwa addinin Musulunci wani kallo na daban.

Ta fuskanci fushi daga wajen iyayenta, wadanda basu shirya jin labarin komawarta Musulunci ba. Amma cikin ikon Allah sai gashi a karshe ba wai iya danginta ba kawai hatta wadanda ba danginta ba sun Musulunci.

Ta nuna musu ainahin menene addinin Musulunci, inda ta nuna musu cewa abinda suke ji game dashi makircine na kafafen sadarwa.

Da taimakon iyayenta, ta samu ta mayar da wani bangare na gidansu ya zama cibiyar addinin Musulunci a kasar, inda ta bukaci duk mai son ya koyi addinin kofa a bude take.

Ta bude wannan cibiya ga wadanda ba Musulmai ba, inda ta bukaci su dinga zuwa a duk lokacin da suke so. A hankali, mutane da yawa suka dinga kai ziyara ciki suna sanin abubuwa da dama game da Musulunci ba wai abinda suke gani a kafafen sadarwa ba.

Sun ji dadin wannan ilimi da suke samu na addinin Allah. Ta ce zama Musulma a wannan lokaci a kasar Turai ba abu bane mai sauki, amma kuma zama Musulmi a lokacin Manzon Allah ma abun babu sauki.

A shekarar 2014, ta samu ta Musuluntar da mutane 1000 a cikin wannan cibiya. Ta samu wannan nasara ne a cikin shekara 8 kawai bayan ta Musulunta.

Yawancin mutanen da suka Musulunta mata ne ‘yan kasar Belgium.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here