Masha Allah: Balarabiya ta tara albashin mijinta da ya rasu na tsawon shekara 30 ta gina Masallaci dashi

0
869

Wata Balarabiya ta nuna tsananin soyayya da juriya, inda ta dinga ajiye albashin mijinta da ya rasu na tsawon shekara 30 ta gina Masallaci da sunan shi.

Irin wannan juriya da wannan baiwar Allah ke dashi ya bawa mutane mamaki. Ta ajiye kudin ba tare da ta taba su ba, sannan ta gina wannan Masallaci da su.

Shin ba abin mamaki bane? labarin matar ya taba zuciyar mutane da dama, bayan dan ta Mohammad Al-Harbi, ya wallafa labarin a shafinsa na Twitter.

Al-Harbi ya wallafa hoton, inda yake da nuni da mahaifiyarsa a tsaye a cikin harabar Masallacin wanda ta gina.

Ya ce: “Bata mori albashin mahaifina ba ko kadan. Ta shafe shekaru 30 tana tara kudin har sai da ta gina Masallaci da sunan mahaifina. Allah ya jikanshi ya saka masa da gidan Aljannah. Daga Allah muke kuma gare shi zamu koma.”

Cikin lokaci kalilan wannan rubut da ya wallafa ya bazu a shafukan sadarwa, inda mutane suka dinga yabawa wannan baiwar Allah.

Wannan labari dai yana da taba zuciya. Mace mai karfin hali irin wannan da ta tara irin wannan kudade domin kawai ta gina Masallaci da sunan mijinta. Ta bar misali wanda ya kamata matan Musulmai suyi koyi da shi.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here