Masha Allah: Ango ya bawa Amarya Qur’ani da ya rubuta da hannunshi a matsayin sadaki

0
439

Muna zaune a zamani da kudi ya maye gurbin kowanne abu na rayuwa. Manyan motoci, manyan gidaje, kayan sawa na alfarma sune abubuwan dake nuni da cewa mutum ya dace a rayuwa.

Yanayin yadda muke aure a wannan lokacin ya wuce gona da iri, domin kuwa almubazzaranci yafi abinda aka ce muyi koyi dashi yawa.

Rayuwar da muke yi a yanzu ba ita ce irin rayuwar da fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW ya koyar damu ba, a koda yaushe yana yi mana nuni da muyi rayuwa mai sauki.

Amma duk da haka akwai mutanen da wannan rayuwa ba ta dame su ba, inda suke iya bakin kokarinsu wajen ganin sun tsarkake dangantaka da soyayyarsu. Wannan yana daya daga cikin labaran da muka zo muku dashi a yau.

Duk da dai bamu da wani cikakken labari akan ma’auratan. Abinda muka sani shine angon ya rubuta Al-Qur’ani mai girma da hannunshi ya bayar dashi a matsayin sadaki ga amaryarshi.

Mutane da yawa baza su yadda a basu Al-Qur’ani a matsayin sadaki ba, musamman yanzu da sadaki ake biyanshi da kudi.

Wannan biki nasu ya zama abin mamaki sosai a yankin su domin kamar sune mutane na farko da suka fara gabatar da irin wannan aure a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here