Dan jaridar yanar gizo me shafin Hausa Media, Aliyu Dalhatu, yayi raddi ga me shafin Jakadiyar Arewa TV, wanda aka fi sani da Jakadiyar Tona Asiri, akan wani rubutu da yayi kan lamarin matashin da ya sha guba saboda bai samu ganin Maryam Yahaya ba.

Bayan fitar labarin shan fiyafiyar da matashin yayi kan Maryam Yahaya ya karade shafukan sadarwa, mai shafin Jakadiyar Arewa TV ya wallafa hoton Maryam din inda yayi rubutu kamar haka:

View this post on Instagram

Wallahi Allah Maryam Yahaya bata da mutunci. Ya mutum zai yi tattaki tun daga Yobe ya zo ganinki amma ki ki saurarsa? Wannan ai hauka ne da rashin sanin mutuncin masoyi. A ce saboda sonki har fiya-fiya bawan Allah ya sha amma ko a kula ta gagara?! Idan yanzu kin ga kina tashe to ki tambayi yau ina Safiya Musa? Ina Fati Muhammed? Ko Mansura Isah da ta auri Sani Danja ina take yanzu? Ban da ma tana aiyukan tallafi wa zai tuno da labarinta? Su Hadiza Kabara kuwa yanzu rara-gefe suke. Duk wadannan an so su fiye da ke. Yan wasan Hausan nan ku dauki kanku ku wani aza girman kan banza da wofi. Haka na ga wani mun shiga rastuwarent a Abuja yana ta wani kobarewa sai ka ce wata tsiya zai yi a gurin. Ke fa ba wani ilimi ne da ke na yabawa ba. Kudin ma wallahi babu. Sai dai hoto a Instagram da dan karan girman kan banza da wofi. In banda ma tuwo ya cika idon yaron ni sai na rasa me ya baro a Yobe ya tafi Kano kallon wannan yarinyar! Shi masoyinka ai naka ne ko daga wani kauye yazo. Kin ganni nan wallahi zan iya haduwa da Messi ko Ronaldo ya yi gaba na yi gaba don basu dameni ba. Amma da muka hadu da Ali Nuhu a jirgi na ga mutane sun shareshi sai da na taso muka tattauna ko don na tuna masa shi “celebrity” ne da bai kamata a nuna masa bai isa ba. To bai kamata kuma idan kun shiga cikin jama’a ku dinga wulakanta wadanda suke nuna kun i sa ba. Follow @mallam_dallah_dallah @mallam_bakwana @wuf_2020 @mata_yan_bariki

A post shared by jakadiyya_arewa_tv 🌀🇳🇬 (@jakadiyyan_arewa_tv_) on

Sai dai kuma ganin wannan rubutu, ya sanya Aliyu Dalhatu ya maida martani ta shafinsa, inda ya ce:

“Zuwa ga Jakadiyar Tona Asiri.

“Yanzu na ga abun da kuka rubuta akan Maryam Yahaya, Allah Sarki wato Bahaushe in ya daukaka kullum shi abun zagi ne a wurin mutane irinku.

“Shin menene laifin Maryam Yahaya? Ita ta sanya aka sha fiya-fiya? Ko ita ce ta sanya shi zuwa nemanta? Abin tausayi ne halin da ya shiga, amma babu dalilin dora mata laifi.

“Kun ce bata da ilimi da kudi shin don Allah a ina tace tana da wadannan? Sannan kun ce bata ziyarce wanda ya sha fiya-fiyan ba, kun yi sauri domin kuwa watakila a yanzu haka ma taje ganinsa domin jiya an tabbatar da yau za ta je ta duba shi!

“Duk kuwa da cewa ra’ayina bai kamata taje ganinsa ba, domin zuwan zai iya karafafawa wadansu masu irin wannan ragon tunanin sake aikata irin makamancin hakan.

“Daga karshe Jakadiya cin mutuncin dan Adam haka sidabban abu ne marar kyau, domin kuwa komai muka aikata a fili ko a Instagram akwai ranar biya!

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here