Malamai sun yi Allah wadai da tone kabarin jikan Sayyadina Umar da ‘yan shi’a suka yi

0
625

Tarayyar manyan Malaman addinin Musulunci na duniya, wadanda aka fi sani da Ulama’u sunyi tir da Allah wadai akan tona kabarin Umar bin Abdul’aziz, wanda yake jika ne a wajen Sahabin Manzon Allah (SAW), Sayyadina Umar, dake birnin Idlib cikin kasar Siriya.

Babban sakataren kungiyar Ali Muhyiddin El-Karadagi shine ya fitar da wata sanarwa, inda yake cewa:

“Wannan abu da suka yi alama ce dake nuna irin girman kiyayyar da suke yiwa Khalifa Umar bin Abdul’aziz, duk kuwa da shekaru 1300 da rasuwarsa.

Sakataren ya kara da cewa mutanen da suka yi wannan aika-aika ta son zuciya ba wai iya Umar bin Abdul’aziz suka ciwa mutunci ba, sun zagi masu bin akidar Ahlul Sunnah ne da ma daukacin Musulmai na duniya baki daya.

Karadagi ya kara da cewa an ci zarafin mataccen ne saboda kawai ana so a tada zaune tsaye sannan a raba kan Musulman duniya baki daya.

Kafafen sadarwa da suke da alaka da gwamnatin kasar Siriya ta Asad sun yi ta wallafa wannan bidiyo na kabarin a lokacin da aka tone shi.

Har yanzu dai ba a san inda mutanen da suka tone kabarin suka nufa da gangar jikin Umar bin Abdul’aziz ba, inda yanzu kimanin sama da kwanaki goma kenan da yin wannan aika-aika.

A watan da ya gabata ne dai muka kawo muku rahoton yadda ‘yan shi’a suka shiga inda kabarin Khalifa Umar bin Abdul’aziz suka tone kabarin shi.

Ku karanta cikakken labarin: ‘Yan shi’a sun tone kabarin Umar bin Abdul’aziz jika a wajen Sayyadina Umar

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here