Makiyan Buhari ne suke son tarwatsa Arewa – Sarkin Katsina

0
4299

Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya ce ya sha sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan yayi hankali da makiyansa da suke tare dashi a gwamnati da kuma wadanda basa cikin gwamnatinsa.

Sarkin ya ce wadannan makiya nashi sune suke so su tarwatsa nahiya arewa baki daya.

Ya bayyana hakane jiya a fadarsa a lokacin da yake yiwa tawagar gwamnatin tarayya da ta kai mishi ziyara jawabi, wacce babban mai bawa shugaban kasa shawara a fannin tsaro, Janar Babagana Monguno ya jagoranta.

Tawagar wacce ta hada da shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa, Mohammed Adamu; shugaban hukumar ‘yan sandan farin kaya DSS, Yusuf Magaji Bichi; da kuma darakta janar na hakumar leken asiri ta kasa, Ahmed Rufai, sun kai ziyarar ne sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga suke kai wa jihar a ‘yan kwanakin nan.

Haka kuma tawagar ta kai ziyarar domin ta kara tabbatar da kokarin da gwamnatin tarayya take yi wajen kawo karshen lamarin na hare-haren a jihar.

Idan ba a manta ba babban mai taimakawa shugaban kasa a fannin sadarwa, Malam Garba Shehu, ya bayyanawa Channels TV a wani shiri da suke gabatarwa mai suna Sunrise Daily, cewar sarakunan gargajiya na jihar Katsina ne suke taimakawa ‘yan bindiga a jihar.

Ya ce sarakunan gargajiyar wadanda bai bayyana sunayensu ba, suna taimakawa ‘yan bindigar su gudu a duk lokacin da jami’an tsaro suke shirin kai musu hari.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here