Mai yasa ba a kira mijina da barawo ba lokacin da yake raye har sai da ya mutu? – Maryam Abacha

0
8502

Maryam Abacha, matar marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja Janar Sani Abacha, ta yi magana akan kudaden da aka karbo daga kasashen ketare da mijinta ya kai can ya boye.

A wata hira da tayi da Kano Focus, a lokacin tunawa da tsohon shugaban kasar karo na 22 a jihar, Maryam ta ce da sannu gaskiyar kudaden da aka ce ana karbowa daga kasashen ketaren za ta fito fili.

Maryam, wacce ta zargi mutanen jihar Kano da cin amanar mijinta ta nuna mamakin yadda aka yi lokacin da yake raye ba a kirashi da barawo ba har sai bayan ya mutu.

Ta ce: “Daga yaya lokacin da yake raye shi ba barawo bane har sai da ya mutu?”

“Shin nawa ne wannan kudi da ya shafe shekaru 22 ana ta faman karbowa?

“Abin kunya ne kuyi karya akan mutumin da bashi da rai! Abin kunya ne kuyi karya akan shugabanku.

“Idan har yayi ba daidai ba Allah yafi kowa sani. Idan ma kuma wasu ne suke dora laifin akan shi, na tabbata komai lokaci ne.

“Komai zai zo karshe za suyi dana sani kamar yadda kasar Amurka take dana sani yanzu. Duka wanda bashi da imani zai zo yayi dana sani, kamar yadda wannan cuta coronavirus ta zo ta kawo karshen duniya.

Ta kara da cewa akwai mutane da yawa da mijinta ya taimakawa a jihar Kano, wadanda a yanzu haka ko gaishe da ita basa yi.

Ta ce: “Yayi aiki a Kano, ya taimakawa jihar Kano, banda haka akwai mutane da yawa da ya taimakawa da a yanzu haka ko gaishe dani basa yi.

“Kawai sun tsane mu ne. Mene dalili? Allah yana nan yana kallo.”

Idan ba a manta ba Press Lives ta kawo muku rahoton da babban dogarin tsohon shugaban kasar Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce duka kudaden da aka karbo daga kasashen wajen Abacha ya boye su ne domin ya kare mutanen Najeriya daga shiga wani hali.

Al-Mustapha yace shawarar ajiye kudaden a kasashen ketaren anyi ta ne tsakanin manya masu fada aji na kasa sarakunan gargajiya na yankin kudu da arewacin Najeriya a wancan lokacin.

Tsakanin shekarar 1998 zuwa 2020, sama da dala biliyan uku da rabi aka karbo a cikin kudaden da Abacha ya boye a kasashen ketaren.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here