Mahaifinmu yafi son shi fiye da yadda yake son na shi yasa na kashe shi – Cewar Ibrahim da ya kashe dan uwansu

0
164

Rundunar ‘yan sandan Najeriya dake karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (DCP) Abba Kyari, ta samu nasarar kama wasu samari guda biyu masu suna Ibrahim Abdullahi mai shekaru 20 da kuma Hassan Amadu mai shekaru 22 da laifin kashe dan uwansu Kadade Abdullahi a kauyen Amana Maikasuwa dake jihar Kaduna.

Saurayin dan shekara 20 da ake zargin yana da hannu a sace-sacen shanu da kuma garkuwa da mutane, rundunar ‘yan sanda ta ‘Operation Puff Adder’ ce ta kama shi.

Bayan gabatar da bincike a kanshi, Ibrahim ya bayyana cewa yana daya daga cikin ‘yan kungiyar da suke fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane. Haka kuma ya bayyana cewa shine ya sanya aka yiwa dan uwanshi fashi da makami sannan aka kashe shi saboda mahaifinsu yafi son shi.

Ibrahim ya ce:

“Mahaifina yana da mata hudu kuma yana da ‘ya’ya da yawa. Ban san me ya gani a jikin Kadade ba da ya saka mahaifinmu baya yi mana komai ba tare da ya nuna bambanci akan shi ba.

“An kai ni makarantar almajiranci a Kaduna, inda shi kuma Kadade aka barshi yayi karatun boko har zuwa sakandare, mahaifinmu ya ce boko ba dole bace a garemu tunda duka manoma yake so mu zama. Amma duk da haka shine yake fara kiran mu jahilai bamu iya turanci ba.

“Daga yaya zan iya turanci bayan mahaifina bai sani a makaranta ba? Abinda na iya kawai shine girbe kayan gona da kuma kiwon shanu. Dole ta sanya nayi aure domin na nuna mishi cewa karfina ya kawo.

“Bayan nayi aure mahaifina ya bani shanu 20 kawai da filaye guda biyu. Abinda yasa na kashe dan uwana ta hanyar taimakon abokanan sana’ata shine, mahaifina ya yarda da dan uwana sosai fiye da yadda ya yadda dani. Haka kuma saboda kudin shanun da mahaifinmu ya sayar N1,700,000, ya bawa dan uwana ajiya.

“Dan uwana ya sayar da shanu kan kudi N1.7m, yayi ta yayatawa. Mahaifina shima yayi murna sosai sai yace masa ya ajiye kudin a wajen shi.

“Munyi tunanin zai raba mana kudin a wannan lokaci, ni kuma wannan rana ina cikin rashin kudi, sai na tambayi mahaifinmu kudi, sai ya fara zagina ya ce naje na koyi yadda ake rayuwa kamar yadda Kadade yake.

“Cikin fushi na kira daya daga cikin ‘yan kungiyar mu, Haruna na sanar dashi game da kudin dake gidan mu. Na ce musu su zo sannan su tabbatar da sun kashe dan uwan nawa.

“Sai dai yanzu ina dana sanin abinda nayi, na yi tunanin mutuwar shi za ta saka mahaifinmu ya bani wasu bangare na kasuwancinsa. Mahaifina bai ji dadi ba sosai, na bashi hakuri na nuna masa cewa haka Allah ya so.

“Da safe na shiga daji domin na hadu dasu mu raba kudin, sai suke gaya mini naira dubu dari uku kawai suka samu a wajen dan uwan nawa, na karbi dubu dari tunda ni ne na samo aikin na bar musu sauran.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here