Mahaifina bai taba tuka mota ba har ya koma ga Allah, amma mutane nayi masa wani kallo na daban – Cewar Amina ‘yar gidan Abba Kyari

0
251

Babbar ‘yar gidan Abba Kyari, Amina ta yi rubutu na girmamawa akan mutuwar mahaifinta, wanda ya mutu sanadiyyar cutar Coronavirus da ta kama shi a ranar 17 ga watan Afrilu.

A cikin rubutun na ta mai suna ‘My Daddy, My Best Friend’ wanda ta wallafa a ThisDay, Amina ta bayyana cewa ‘yan Najeriya ne basu fahimci ko wanene mahaifinta ba suke yi masa wani kallo na daban, duk kuwa da irin kokarin da ya yiwa Najeriya wajen gina ta.

Ta ce tunda yake bai taba tuka mota ba har ya mutu, bama tuki ba ko koyon tuka mota bai taba yi ba.

Ta ce mahaifinta bai taba fitowa yayi magana akan masu zagin shi ba, saboda yana ganin hakan zai dauke masa hankali daga abinda ya sanya a gaba na ganin cigaban Najeriya.

Amina ta ce ta san rasa mahaifi ba karamin tashin hankali bane, amma kuma bayan mutuwar ta shi mutane kowa ya dinga fadar abinda yazo bakinsa wannan shine babban abin takaici.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here