Maganar gaskiya Abacha bai saci kudin Najeriya ba, hasali ma ya boye kudin ne daga fadawa hannun Turawa – Buba Galadima

0
153
  • Buba Galadima ya bayyana cewa tsohon shugaban mulkin soja Sani Abacha, bai saci kudin Najeriya ba
  • Galadima ya ce Abacha ya boye kudin ne domin ya hana Turawa sace wa
  • Fitaccen dan siyasar ya bayyana cewa Abacha yayi hakane bayan shawarar da Saddam Hussein da Muammad Gaddafi suka bashi a wancan lokacin

Fitaccen dan siyasa, kuma daya daga cikin masu kalubalantar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya bayyana dalilan da ya saka tsohon shugaban mulkin soja, Sani Abacha ya boye biliyoyin daloli na Najeriya a kasashen waje.

Tun daga kan mulkin Obasanjo, Najeriya na karbo biliyoyin daloli da ake zargin Abacha ya sace ya boye a kasashen waje.

A ‘yan kwanakin nan ne gwamnatin shugaba Buhari ta samu nasarar karbo dala miliyan 311 da Abacha ya boye.

Sai dai kuma a wata hira da yayi da The Nation, Buba Galadima ya ce Abacha bai saci kudin Najeriya ba kamar yadda aka sanya duka ‘yan Najeriya suka yadda da hakan.

Galadima ya ce, Abacha ya boye kudin a kasar waje ne a lokacin da kasar Amurka ke shirin sanyawa Najeriya takunkumi.

Ya ce tsofaffin kasashen duniya ne suka shawarci Abacha ya boye kudaden a kasashen waje, saboda koda kasar Amurka ta cigaba da yiwa Najeriya barazana hankalin mutane ba zai tashi ba.

Cikin shugabannin da suka shawarci Abacha a cewar Galadima akwai Saddam Hussein da kuma Muammar Gaddafi.

“Na sani a wancan lokacin Abacha da ya riga ya san duka masu yi masa aiki a gwamnati, a lokacin manyan shugabannin kasashen duniya ne suka shawarceshi akan ya boye kudin.

“Saddam Hussein yana daya daga cikinsu, Muammar Gaddafi na daya daga cikinsu. Sun shawarceshi akan akwai yiwuwar kasar Amurka ta sanyawa Najeriya takunkumi, saboda haka sai suka shawarce shi ya boye kudade a kasashen duniya da zai dauki Najeriya tsawon watanni shida bata sake neman kudi ba, koda kuwa ace Amurka ta rufe asusun Najeriya baki daya.

Galadima ya ce yana daya daga cikin wadandan suka yi aiki a karkashin Abacha. Ya ce yadda mutane suka dauka cewa Abacha ya saci kudin Najeriya suna yi ne a bisa rashin sani.

Da yake magana akan kudin da aka karbo daga kasashen wajen, Galadima ya kalubalanci gwamnatin Buhari akan yadda za ta kashe kudin.

Ya ce mai magana da yawun shugaban kasa wanda bai fito ya bayyana sunanshi ba ya ce za ayi amfani da kudin wajen bayar da tallafi ga talakawa, sai kuma gashi alkalin alkalai na tarayya, Abubakar Malami, ya ce za ayi amfani da kudin wajen gina abubuwan more rayuwa.

Buba Galadima ya ce dole sai gwamnatin Najeriya ta tuntubi majalisar tarayya kafin ta fara amfani da kudin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here