Mafitsarar wani dan giya ta barke bayan ya shanye kwalba 10 ta barasa

0
437

A farkon watan nan wani mutumi da aka bayyana sunan shi da Mr. Hu, ya shanye kwalba goma ta barasa, kafin ya dawo sai bacci mai nauyi ya dauke shi, yaya aka yi sai ya kasa tashi yayi fitsari bayan shanye wannan uwar giya.

Likita ya bayyana cewa Mr Hu bai ji alamu na yin fitsari ba a lokacin da yake baccin. Sai dai kuma komai ya canja bayan ya tashi daga baccin.

A wani rahoto da aka ruwaito a ranar 18 ga watan Yuni, likitoci a asibitin Zhuji dake garin Zhejiang, ya bayyana cewa marar lafiyan bayan ya tashi daga bacci ya bayyana cewa yaji wani irin zafi mai tsanani a cikin shi. Ya ce a lokacin da aka saka shi a cikin motar asibiti radadin ya cigaba da ya kai ga ko iya kwanciya baya yi.

Sai dai bayan zuwa asibiti likitoci sun bayyana dalilin wannan radadi da yake ji na da nasaba da mafitsararsa da ta tsage gida uku.

Daya daga cikin wuraren da ya tsage ya taba cikin cikinsa, inda ya sanya daya daga cikin hanjin shi ya shiga cikin mafitsarar ta shi. Hakan ka iya sanadiyyar mutuwarshi idan aka barshi ba tare da anyi masa aiki ba.

Daga baya wasu likitoci sun hadu sun yi masa tiyata, inda suka gyara mafitsarar ta shi, yanzu haka dai Mr Hu da yake da shekaru 40 ya samu lafiya.

Likitocin sun ce duk da dai yana wuya a samu irin wannan lamari na Mr Hu, amma akwai yiwuwar hakan zai iya faruwa da kowa. Mafitsarar mutum kamar roba ce tana iya budewa idan ruwa yayi yawa a cikinta, amma tana iya daukar yawan fitsari mililita 450 zuwa 500, shan giya na bukatar mutum yaje yayi fitsari sosai ba kamar mutum idan ya sha ruwa ba.

Likitoci sun ce jikin mutum na daukar awa 10 kafin ya fitar da kofi biyu na fitsari, hakan shine iya yadda mutum zai iya tsayawa ba tare da yayi fitsari ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here