Ma’aikacin NEPA ya yiwa karamar yarinya fyade a Abuja ta haihu, sannan ya kwace jaririn ya jefar

0
1309

Wani ma’aikacin wutar lantarki mai suna Nura Salisu dan shekara 30 a duniya ya shiga hannun rundunar ‘yan sanda ta Abuja, bayan an kama shi da laifin yiwa yarinya ‘yar shekara 16 mai suna Nanket Manasseh cikin shege, ya kuma karbi jaririn yaje ya jefar a wani waje da babu wanda ya sani.

Mutumin wanda ya fara lalata da yarinyar tun tana ‘yar shekara 15, ya shiga hannun ‘yan sanda a ranar 22 ga watan Mayu da laifin sace jaririn mai watanni 6 kacal a duniya kuma yaki ya bayyana inda yake.

Da take bayani ga ICIR, Manasseh ta ce, jami’in wutar lantarkin yayi ta kokarin kwanciya da ita tun tana ‘yar shekara 10. Ta bayyana yadda ya siyo mata wayar salula a lokacin da take aji uku na firamare, yarinyar ta ce yayi mata fyade ta hanyar yi mata wayo ya kai ta otel a Jahi, inda yace mata yana da wani abu mai muhimmanci da zai gaya mata.

Ta ce;

“Na ce masa ba zan iya kwanciya dashi ba, amma yayi mini fyade ya fita ya barni a wajen. Da safe na kwashe kayana na tafi gidan ‘yar uwata ba tare dana sanar da wani abinda ya faru ba.”

Nanket Manasseh Photo Source: Linda Ikeji Blog

Bayan sun kira Salisu bayan sakamakon asibiti ya fito na cewa tana dauke da ciki, Manasseh ta ce, Salisu ya bawa matar da take zaman riko a hannunta ka’idoji akan karbar jaririn. Ya ce zai amince ya karbi jaririn ne kawai idan har ta haihu a watan Nuwambar shekarar 2019.

Sai dai kuma bayan ta haihuwa a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2019, Manasseh ta ce Salisu ya fara fushi da ita a duk lokacin da tayi kokarin kiran shi ya kawo abinda za ta dauki nauyin jaririn da shi. Abubuwa sun kara dagulewa ga budurwar bayan jaririn ya fara rashin lafiyar hakori, sai ta kira Salisu a ranar 21 ga watan Mayu. Sai ta ce Salisu yaje sun hadu da ita inda ya karbe jaririn ta karfin tsiya ya tafi dashi.

Manasseh ta bayyana haka cikin kuka;

“Salisu ya kwace jaririn ta karfin tsiya. Nayi kokarin kwatar jaririn amma ya tafi dashi. Har yanzu ban kara saka idona akan jaririn ba, kuma koda muka kara haduwa dashi bai sanar dani inda ya ajiye jaririn ba.”

An kai karar Salisu ne a ofishin ‘yan sanda na Jahi kafin aka danka lamarin zuwa ofishin ‘yan sanda na Mabushi washe gari. Bayan an kama shi anyi masa tambayoyi, Salisu ya bayyana wurare uku da jaririn yake.

Nanket and Salisu Baby Photo Source: Linda Ikeji Blog

Da farko yace ya ajiye jaririn a cikin Jabi Lake ne, daga baya kuma ya ce ya bawa abokinshi mai suna Moses wanda ya tafi dashi Kano a ranar da ya bada shi. Salisu ya kara da cewa yazo kuma ya daina samun abokin nashi a waya, kuma bai san inda yake zaune ba a Kano.

Daga baya kuma Salisu ya ce ya kaiwa ‘yar uwarshi jaririn ne wacce take zaune a Garki, amma da aka tambayeshi ya kai ‘yan sanda gidan ‘yar uwar tashi sai yaki yadda.

Bayan lamari yayi kamari akan inda jaririn yake, an danka Salisu zuwa ofishin CID na Abuja domin cigaba da bincike akan shi.

DPO na ofishin ‘yan sanda na Mabushi, SP Bello Sa’adu, ya ce babban abinda yafi damunsu shine su nemo inda jaririn yake, inda daga baya kuma sai a yankewa Salisu hukunci.

Wani dan uwan Manasseh mai suna Lere P. Samuel, ya bayyana cewa Salisu ya kai ‘yan sandan inda yace musu ya ajiye jaririn amma da aka duba babu komai a wajen a ranar Juma’a 29 ga watan Mayu.

Ya kara da cewa daga baya mataimakin sufeton ‘yan sanda na kasa ya tilasta shi ya bude wayarshi, bayan anyi ta fama da shi yaki yadda ya bude.

Har ya zuwa yanzu dai wannan ma’aikacin wutar lantarki yana hannun jami’an tsaron kuma ana cigaba da bincike a kanshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here