Lokaci yayi da za a daina kashe Musulmai a kasar Indiya – Dan kasar majalisar Birtaniya

0
2191

Bacin ran abinda gwamnatin kasar Indiya ke yiwa Musulmai na kara karuwa a duniya. Manyan kungiyoyi na duniya sun fara magana akan wannan al’amari, inda suka fara aika sakon kai tsaye zuwa kasar akan a daina kashe Musulmai a kasar cikin gaggawa.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) tuni sun yi Allah wadai da wannan kisan kiyashi da gwamnatin kasar ke yiwa Musulmai a ‘yan kwanakin nan.

Da yake tofa albarkacin bakinsa shi ma, akan abinda ke faruwa a kasar ta Indiya, dan majalisar kasar Birtaniya, Steve Baker, ya nuna bacin ranshi matuka akan nuna kyamar Musulmai da gwamnatin kasar Indiya ke yi, inda ya bukaci suyi gaggawar dakatar da kisan kiyashin da suke yiwa Musulmai.

Steve Baker dan majalisar kasar Birtaniya da yayi kira da a daina kashe Musulmai a Indiya

Steve Baker ya ce: “Akwai kwararan shaidu dake nuni da cewa ana kashe Musulmai a kasar Indiya. Wannan cin zarafi ne da rashin imani, kuma ya kamata gwamnatocin kasashen duniya su sanya baki akan wannan rashin imani da ake yi. Ni bawai ina kalubalantar mutanen Indiya bane, amma abinda nake so na fada shine gwamnatin kasar na nuna kyamar addinin Musulunci a fili ta hanyar kashe su basu ji ba basu gani ba, saboda haka dole ne ta daina, kuma nayi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta hakkin da aka dora mata na kare al’umma.

Da yake wallafa bidiyon Steve Baker a shafinsa na Twitter, fitaccen mai fafutukar kare hakkin dan adam na kasar Kuwait, Mejbal Al-Sharika, ya gargadi gwamnatin kasar Indiya da rubutu cewa; “Hakurin mutanen duniya ya fara karewa akan mulkin nuna bambanci da ake yi a kasar Indiya.”

Sharika dai tuni ya riga Majalisar Dinkin Duniya nuna adawa akan wannan abu dake faruwa a kasar ta Indiya, inda kuma ya bukaci majalisar dinkin duniyar da ta fito ta dauki mataki cikin gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here