Labarin mutuwar jaruma Fati Baffa Fagge ya tada hankalin ‘yan Kannywood

0
2182

A jiya Litinin ne 15 ga watan Yuni aka tashi da labari marar dadin ji na rasuwar Jaruma Fati Baffa Fagge, wanda aka dinga yadawa a kafafen sada zumunta musamman Facebook, inda hankalin ‘yan uwa da abokanan arziki da masoyanta ya tashi bayan jin wannan labari.

Sai dai kuma bayan fitar wannan labari, abokin sana’arta jarumi Ali Rabi’u Ali, wanda aka fi sani da Daddy, ya kira lambar wayarta domin yaji gaskiyar abinda yake faruwa.

Abin mamaki yana kira kuma sai ji yayi ta daga wayar, ga dai yadda tattaunawar ta su ta kasance:

Da daga wayar ta, sai ya fara da tsokanar ta da cewa: “Fati marigayiya,” cikin dariya ta amsa da cewa: ‘lallai kuwa Fati marigayiya,” jaruman sun cigaba da magana inda suka nuna rashin jin dadinsu akan yadda mutane ke yada labari na kanzon kurege babu gaira babu dalili.

Jarumin ya ce: ‘Kawai sai dai kaji wane ya mutu wane yayi kaza,” ita kuwa ta nuna mamakinta ta ce; “wai har da cewa za ayi jana’iza ta karfe 10.”

Ta ce tunda ta tashi da safe ta samu kiran waya yafi guda 100, ta kara da cewa tunda ta dauki wayarta bata ajiye ba, domin kuwa hatta cajin wayarta ya kusa karewa.

Ta ce bata san dalili ba haka kawai mutum yana zaune a dagawa ‘yan uwanta da abokanan arziki hankali, inda shi kuma jarumin ya tabbatar mata da hakan babu dadi ko kadan.

Jarumar ta ce wallahi duk wanda yayi mata wannan abu bata yafe masa ba, domin kuwa ko ba ita ba, ya dauki hakkin ‘yan uwanta da abokanta, ta ce wasu suna kiran wayar kafin su fara cewa komai kuka suke rushewa da shi.

Jarumin a karshe ya bata shawara akan tayi bidiyo ta tura ta sanar da jama’a cewa tana nan da ranta, kuma idan lokaci yayi kowa ma zai tafi.

Ga sautin muryar ta su a cikin wani bidiyo da shafin Tsakar Gida na Youtube ya wallafa:

To Allah dai ya kyauta.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here