Labari mai dadi: Za a bude Masallacin Harami dana Madina don Musulmai su cigaba da ibada

0
159

An gama shiri tsaf domin bude Masallacin Harami dana Madina domin mutane su cigaba da bautar Allah bayan kulle Masallatan da aka yi na tsawon lokaci.

An wallafa wannan rahoto ne a shafin Facebook na Haramain Harifain da kuma shafin Twitter cewa Masallatan guda biyu za a bude su nan ba da dadewa ba.

NEWS | The Ministry of Hajj and Umrah has announced that keeping commitment to relevant procedures, Masjid Al Haram and…

Posted by Haramain Sharifain on Tuesday, April 28, 2020

Wannan labari mai dadi dai ya zo ne bayan ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta bayyana rahoton bude Masallatan guda biyu bayan kammala tsaftace su da aka yi da magunguna, sannan kuma za a gabatar da gwaji akan duk wanda zai shiga don tabbatar da cewa baya dauke da cutar Coronavirus.

Kasar ta Saudiyya dai ta rufe duka Masallatan guda biyu na Makkah dana Madina bayan bullar cutar Coronavirus a kasar, inda ta hana aikin Hajji dana Umrah, da kuma gabatar da sallar Tarawihi da Tahajjud a cikinsu.

Hukumomin lafiya na kasar ta Saudiyya suna daukar kwakkwaran mataki akan masallatan, amma duk da haka sun bayyana cewa baza a gabatar da sallar tarawihi da da sallar idi, saboda a wadannan lokutan mutane na tururuwar zuwa Masallatan.

Wannan dai labari ne mai dadi ga duka Musulman duniya idan suka ji cewa za’a bude Masallatan guda biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here