Labari mai dadi: Sojojin Najeriya sun ceto yara da mata 241 daga hannun ‘Yan Boko Haram

0
4472

Rundunar sojin Najeriya ta ‘Operation Lafiya Dole’ sun samu nasarar ceto yara da mata 241 da ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa da su a kauyen Mudu dake jihar Borno.

A wata sanarwa da helkwatar tsaro ta fitar a yau Alhamis 28 ga Mayu, ta ce sun samu nasarar kwato mutanen da ‘yan bindigar suka sace a harin da suka kai a ranar 23 ga watan Mayu.

Mutanen da sula ceto sun hada da mata 105 da kuma yara 136. Haka kuma sanarwar ta kara da cewa sun samu nasarar kashe ‘yan Boko Haram 12 a harin da suka kai.

A wani rahoto makamancin haka, rundunar soji ta bataliya 151 ta samu nasarar kashe ‘yan Boko Haram din a ranar 24 ga watan Mayu a lokacin da suka yi musayar wuta tsakaninsu da ‘yan bindigar a yankin Firgi dake jihar.

Haka bataliya ta 155 ita ma ta ce ba za a barta a baya ba, inda suma suka kai hari kan ‘yan Boko Haram din da suka gudu dajin Sambisa. Sojojin sun samu nasarar kashe ‘yan bindigar guda biyu, sannan sun samu nasarar kwace makamai masu yawan gaske.

Ga dai wasu daga cikin hotunan wannnan hari da suka kai da kuma mutanen da suka ceto daga hannun ‘yan ta’addar:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here