Labari mai dadi: Sojoji sun kashe sama da ‘yan Boko Haram 343 da kuma ‘yan bindiga 153

0
145

A jiya ne ma’aikatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa tsakanin ranar 18 ga watan Maris zuwa 5 ga watan May, rundunar tsaron Najeriya ta kashe sama da ‘yan kungiyar Boko Haram 343 a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Manjo Janar John Enenche, ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.

Ya ce da yawa daga cikin ‘yan ta’addar kuma sun samu munanan raunika; inda kuma wasu daga cikinsu har da manyan su sun mutu a lokacin harin.

Enenche ya ce sun tarwatsa da yawa daga cikin sansanin ‘yan ta’addar, inda kuma suka kama mutane 16 daga cikin masu kai musu rahoto a lokacin.

A cewarsa sanadiyyar wannan hare-hare da suka kai wasu daga cikin jami’an tsaro sun riga mu gidan gaskiya, inda wasu kuma suka ji raunika.

“Kauyuka da yawa da ‘yan ta’addar suka kai wa hari, sojojin mu sun kwato, yanzu haka kuma komai ya koma daidai.

“Bayan wani bincike da muka gabatar akan ‘yan ta’addar mun gano wuraren da suke buya da kuma abubuwan da suke yi.

A daya bangaren kuma, Enenche ya bayyana cewa rundunar hadin guiwa ta ‘Operation Hadarin Daji’ suma sun samu gagarumar nasara a jihohin Katsina da Zamfara a tsakanin wannan lokaci.

Ya ce sojojin sun tarwatsa sansanin ‘yan bindigar da dama ta hanyar kai musu hari ta sama da kasa, inda suka samu nasarar kashe mutane 146 a jihohin guda biyu.

Ya kara da cewa sun kuma samu nasarar ceto mutane 17 da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su, sannan sun kwace makamai masu yawan gaske a hare-haren.

Haka kuma yace jami’an tsaron sun samu nasarar kwato shanaye 922 da kuma akuyoyi da tinkiyoyi guda 446, sai dai kuma yace sojoji guda hudu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon wannan hari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here