Labari mai dadi: Gwamnatin Buhari za ta dauki mutum 774,000 aiki a fadin Najeriya a watan Oktoba

0
275

A jiya Laraba ne Ministan ayyuka na Najeriya, Festus Keyamo, ya ware kwamiti da za ta dauki mutane 774,000 aiki a fadin Najeriya, karkashin tsarin Ayyuka na Musamman wato Special Public Works (SPW).

Kwamitin wacce darakta janar na daukar ayyukan yi na Najeriya, Mohammed Nasir Ladan Argungu, yake jagoranta.

SPW dai yana daya daga cikin tsare-tsaren shugaban kasa Muhammadu Buhari na samawa mutane aiki a Najeriya. Tsarin zai bawa kowacce karamar hukuma dake Najeriya damar fitar da mutane 1,000 domin basu aikin, inda za su yi aikin cikin watanni uku daga watan Oktoba zuwa Disambar 2020.

Keyamo ya ce ma’aikatan za a dinga biyansu naira dubu ashirin (N20,000) a kowanne wata.

Ya ce shugaban kasar yana neman ‘yan Najeriya ne, ba wai za ayi duba da jam’iyya ko bangaranci bane.

Ya ce shugaban kasar zai sauke duk wani mutumi da yaga yana kokarin yin ha’inci wajen daukar ma’aikatan.

Argungu ya ce za a bayyana yadda za a dauki ma’aikatan nan ba da dadewa ba.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here