Kyamar Musulmai: An harbe kyakkyawar budurwa Musulma a kasar Ingila dauke da azumi a bakinta

1
204
  • Wani lamari mai daga hankali ya faru a kasar Ingila, inda wani mutumi da har yanzu ba a san kowaye ba ya harbe wata budurwa Musulma da tsakar rana
  • Ana zargin mutumin dai yana daya daga cikin masu kyamar Musulmai da aka saba samu a kasar ta Ingila
  • Mutumin dai ya arce bayan ya harbi budurwar a bakin wani shagon sayar da kaya

Wani lamari mai tada hankali ya faru a Blackburn Lancashire, dake kasar Ingila, inda wani mutumi ya harbe wata kyakkyawar budurwa Musulma mai shekaru 19 a duniya a lokacin da take fito daga wani shagon siyayya.

Lamarin ya faru da ranar Allah a ranar Lahadi a bakin shagon.

Budurwar mai suna Aya Hachem, ‘yar asalin kasar Labanon dake zama a kasar ta Ingila, taje shagon ta sayi kaya, inda a lokacin da take shirin tafiya gida wani mutumi a cikin mota mai kirar Toyota Avensis ya harbe ta, an garzaya da ita asibiti, amma Allah ya karbi ranta a asibitin.

Kyakkyawar budurwa Aya Hachem wacce aka harbe a kasar Ingila (Lancashire Police)

Mutumin ya gudu bayan ya kasheta. ‘Yan sanda sun fara daukar mataki akan lamarin, jami’in dan sanda Jonathan Holmes, daya daga cikin masu gabatar da bincike akan lamarin ya ce: “Wannan abu ne marar dadin ji da kuma rashin hankali, wanda yayi sanadiyyar rasa rayuwar budurwar.”

‘Yan sanda suna neman wanda ya kashe budurwar, kuma sun nemi taimakon mutanen dake yankin. Jami’in dan sandan ya bukaci mutanen yankin da su fito su taimaka musu wajen nemo wanda ya kashe budurwar, inda yace ya tabbata wani daga cikin mazauna wajen yaga lokacin da mutumin ya gudu.

Motar da mutumin ya kashe budurwar da ita an sameta a wani wuri daban, inda ‘yan sanda ke cigaba da bincike.

Wannan dai ba shine karo na farko da ake kaiwa Musulmai hari ba a kasar Ingila. An kai hare-hare da dama a kasar ta Ingila inda yawanci Musulmai ake kashewa ko kuma aji musu muggan raunika.

Jaridar Press Lives tana mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wannan baiwar Allah, kuma muna rokon Allah ya jikanta ya sa ta huta.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here