Kyamar Addinin Musulunci: An rataye kan alade a bakin kofar Masallaci a kasar Jamus

0
234

Wasu mutane biyu da ba a san ko su waye ba sun rataye kan alade a bakin kofar Masallacin Fatih a ranar Asabar da daddare, a birnin Vaihingen dake kudancin kasar Jamus.

Wariyar launin fata da kyamar addinin Musulunci na cigaba da karuwa a yankin Turai, inda abin ya kai har a cikin watan Ramadana ma basu ja da baya ba.

“Cin mutunci a wajen bautar mu a kasar Jamus shine babban misali. Cewar ministan kasashen waje na kasar Turkiyya, Mevlüt Çavuşoğlu, wanda yayi Allah wadai da wannan hari da aka kai Masallacin na kasar Jamus, inda ya kira hakan a matsayin babban misali na wariyar launin fata da kuma kyamar addinin Musulunci.

A shekarar 2019, an aika da wata takarda wannan Masallaci, inda aka zagi addinin Musulunci, aka zagi Turkawa da kuma Larabawa duka a cikin takardar hadda hoton alade.

Hare-haren da ake kaiwa Masallatai na kara yawa a kasar Jamus, sannan ana kara samun karuwar wariyar launin fata da kuma kyamar addinin Musulunci a yankin na Turai musamman kasar Jamus.

Sai dai kuma a daya bangaren akwai wanda suke nuna goyon bayansu ga mabiya addinin Musulunci dake zaune a kasar ta Jamus, inda idan ba a manta ba a makon da ya gabata Press Lives ta kawo rahoton yadda coci ta bude kofa ga Musulmai suka shiga suka yi sallar Juma’a a ciki yayin da gwamnati ta kulle Masallatai saboda cutar Coronavirus.

Haka kuma shugaban kasar Jamus din ya yiwa Musulmai godiya da irin goyon bayan da suka bayar wajen yaki da cutar coronavirus a watan Ramadana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here