Kyakkyawar budurwa ‘yar kasar Japan ta Musulunta saboda kyawun halayyar Musulmai

2
4391

Wata kyakkyawar budurwa ‘yar kasar Japan mai suna Risa Mizuno ta karbi addinin Musulunci saboda kyawun halayyar wasu Musulmai da ta zauna da su.

A watan Nuwambar shekarar 2015 ne ta Musulunta bayan mijin da ta aura ya nuna mata yadda addinin Musulunci yake.

Risa daliba ce a kasar Malaysia tayi kwanaki uku a gidan wasu Musulmai a birnin Kuala Lumpur. Tayi mamakin saukin kai da kyakkyawar dabi’a da wadannan Musulmai suke da ita.

Hoto: Muslimah Tokyo Facebook Profile

Tun bayan Musuluntar Risa tana yin azumi a kowanne watan Ramadana a kasar Japan. Sannan tana yin sallah a birnin Tokyo. Haka kuma tana sanya Hijabi tana kuma alfahari da addinin Musulunci.

Haka kuma Press Lives ta kawo muku rahoton wani saurayi mai suna Anthony Michael ya nuna farin ciki da jin dadi bayan ya shigo addinin Musulunci.

Anthony ya bayyana cewa tun da yake bai taba jin dadi da annushuwa a zuciyarshi ba kamar lokacin da ya karbi kalmar shahada.

Hoto: muslimahtokyo.com

Saurayin ya wallafa hotunan da ya dauka a lokacin da ya karbi addinin Musulunci a shafinsa na Twitter, inda ya yiwa ‘yan uwa Musulmai maza da mata godiya akan yadda suka dinga aika masa da sakonni akan wannan baiwa da Allah yayi masa ta karbar kalmar tsira.

Ga dai labarin a kasa: Matashin Saurayi da ya Musulunta a watan Ramadana ya bayyana irin jin dadi da shauki da ya tsinci kanshi a ciki

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here