Kwarankwatsa ta kashe mutane 116 a Indiya

0
414

Ruwan sama mai karfin gaske da aka tafka a yankuna daban-daban na kasar Indiya, yayi sanadiyyar mutuwar mutane 116, sakamakon kwarankwatsa da ta fado musu.

A wani rahoto da jaridar India Today ta ruwaito, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Bihar ta kasar ta Indiya ta fitar da sanarwar mutuwar mutum 92, inda kuma mutane 20 suka ji raunika, sanadiyyar wannan kwarankwatsa da ta fado kansu a yayin da ake ruwan saman kamar da bakin kwarya.

Ita kuwa jihar Uttar Pradesh ta ce mutum 24 suka riga mu gidan gaskiya, sannan mutane 12 suka ji raunika duka dai sanadiyyar fadowar wannan tsawa.

Bayan asarar rayukan kuma, gidaje masu yawan gaske sun lalace sanadiyyar wannan ruwan sama da aka tafka.

Haka a Najeriya ma, jami’an hukumar kiyaye hadura na Najeriya guda uku sun ce ga garinku nan bayan kwarankwatsa ta fado musu a jihar Ogun dake Kudancin Najeriya.

Lamarin ya faru a safiyar ranar Laraba, 17 ga watan Yuni, a wani kauye mai suna Ilese dake karamar hukumar Ijebu North-East cikin jihar ta Ogun.

Kwarankwatsar ta fado kansu da misalin karfe 10 na safe, yayin da jami’an hukumar ta kiyaye hadura suke shirin fita wajen aiki.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here