Kwana 2 da haduwa, auren wasa na shirin zama gaskiya

0
472

Wani al’amari mai kama da wasan kwaikwayo ya faru a garin Kontagora dake jihar Neja, wanda yake dab da tabbata ya zama gaskiya, al’amarin da aka fara a matsayin wasa a ranar Litinin yanzu ya kai ga sanya ranar daurin aure, inda a gobe Asabar ake shirin daura musu aure a garin Libele.

Jamilu da Nasiba sun hadu a garin Kontagora a ranar farko, inda ‘yar karamar muhawara ta kaure tsakaninsu akan al’amarin da ya shafi aure, wanda take ganin ba zai iya auranta ba, shi kuma yasha alwashin zai iya aurenta muddin tace tana son shi duk da bai shirya yin aure ba.

Nasiba ta amsa da cewa ita fa da gaske take yi kuma ta amince za ta aure shi, nan take abokai suka hada kudin sadaki kuma aka tunkari iyayenta suma iyayen suka amince tare da murna da jin hakan, inda yanzu al’amarin ya kankama ake shirin shan biki.

Yanzu haka dai abokanan ango har sun tanadi dakin da za’a sanya amarya tare da cigaba da shirye-shiryen shagulgulan biki, yayin da suma bangaren amarya suke cigaba da nasu hidimomin akan auren.

Daga haduwar su zuwa ranar daurin auren kwanaki biyar, kuma yanzu sun tabbatar da suna son junan su tsakani da Allah.

Wanda ya bayar da rahoton, Comrade Zakari Y Adamu Kontagora, wanda Tashar YouTube ta tsakar gida ta wallafa a shafinta, ya bukaci jin ta bakin jama’a akan tsakanin Angon da Amaryar waye ya tsinci dami a kala?

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here