Mashahuriyar mata ‘yar kasar Rasha, Marina Balmasheva ta sanar da daukar ciki tare da dan da ta raina mai shekaru 20 a duniya, bayan ta rabu da mahaifin yaron mai shekaru 45.
A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Intagram da take da mabiya sama da mutane 411,000, ta nuna cewa ita da mijin nata kuma dan data raina mai shekaru 20, mai suna Vladimir Vova Shavyrin, suna sa ran samun jariri, inda ta ce ta gaji da boye-boye akan cikin da take dauke da shi.

“Na san nayi gaggawa, har yanzu sakamakon gwajin da aka dauka bai fito ba, amma kawai ina so ku sani tun yanzu. Komai mai yiwuwa ne a wannan duniyar. Muna da cikin mako hudu. Hakan ne yasa muka yanke shawarar aure.“
Labarin masoyan dai yayi ta yawo a kafafen sadarwa bayan Balmasheva ta wallafa hotunanta lokacin tana shekara 22 shi kuma Vladimir yana shekara 7 a duniya.
Da yake magana akan abinda ke tsakanin dan nashi da tsohuwar matarshi, Alexey ya ce:
“Ta yaudari dana, Vova ba zai iya wannan abu ba. Ko budurwa bashi da ita.
“Ko kunya basa ji suna jima’i a gabana idan ina gida. Zan iya yafe mata inda ace kamar ba da dana take yi ba. Tana guduwa dakin dan nawa da daddare idan ina bacci.
“Bayan ta gama lalata da shi za ta dawo kan gado ta kwanta kamar komai ba faru ba. Dana gano ainahin abinda ke faruwa sai na bukaci mu raba auren.”
Dubunnan mabiyanta sun nuna rashin jin dadinsu akan wannan abu da tayi. Wani cewa yayi: “Abinda yake bani mamaki shine wannan yaron ya girma a gabanta ne fa.”
Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:
Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa
Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com