Kuyi watsi da matsin lambar iyayen yara kan bude makarantu – Gwamnatin tarayya ta gargadi gwamnoni

0
400

A jiya Litinin ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta gargadi gwamnatocin jihohi akan suyi watsi da matsin lambar da iyayen yara ke saka musu akan bude makarantu.

Karamin ministan ilimi, Mr Chukwuemeka Nwajiuba, a yayin bayani ga kwamitin gudanarwa ta cutar COVID-19 a jiya Litinin, ya ce bude makarantu a wannan lokacin ka iya kara ta’azzara annobar ta COVID-19 a Najeriya.

Ya kara da cewa ma’aikatarshi bata bawa jihar Oyo damar bude makarantu ba.

Nwajiuba ya ce daliban ajin karshe da suke shirin rubuta jarrabawar kammala makarantar sakandare ta WAEC da NECO, za a kyalesu su rubuta jarrabawar kwanan nan.

Ya roki iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su cigaba da hakuri da bin dokar gwamnati a yayin da take kokari wajen tabbatar da lafiyar al’umma kafin ta bari dalibai su koma karatu.

Haka kuma Nwajiuba ya bukaci iyaye da suyi kokari su tabbatar da lafiyar ‘ya’yansu a gidajensu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here