Kuyi hakuri na gaza cika alkawuran dana dauka na kare rayuka da dukiyoyin ku – Masari ya roki mutanen jihar Katsina

0
4139

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa ya gaza kare rayukan mutanen jihar Katsina daga hare-haren ‘yan bindiga.

Gwamnan ya bayyana hakane makonni kadan bayan hare-haren da ‘yan bindigar suka kai a kauyuka daban-daban na jihar, wanda ya jawo mutane suka dinga fita zanga-zanga a jihar.

Da yake magana da manema labarai a gidan gwamnatin jihar, Masari ya ce baya jin dadi kwata-kwata saboda al’ummar jiharsa basu san wani dadi na mulki ba tun bayan lokacin da ya hau mulkin jihar.

Ya ce ‘yan bindigar sun fi dabbobi rashin imani, saboda suna kashe mutane haka kawai ba tare da wani laifi ba.

Ya ce: “Ba zan iya hada ido da su ba, saboda mun kasa kare rayukansu, kamar yadda muka dauki alkawarin kare rayukansu da dukiyoyinsu a jihar.

“Ban taba tunanin haka halayen mutanen da suke zaune a daji yake ba, ‘yan bindigar da rashin imaninsu yafi na dabbobi.

“A daji, zaki ko damisa na kisa ne kawai idan suna jin yunwa, kuma ba wai duka dabbobi suke kashewa ba, tana kashe wanda za ta iya ci ne kawai a lokacin.

“Amma abinda yake faruwa a nan shine, ‘yan bindigar za su shiga gari su fara harbin kan mai uwa da wabi ba tare da wani dalili ba, kamar dai hari da suka kai a Faskari dake cikin karamar hukumar Dandume.”

Idan ba a manta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari a ‘yan kwanakin nan ya tabbatarwa da mutanen jihar ta Katsina akan shirin da gwamnati tayi na tabbatar da tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane a jihar dama sauran jihohi a kasar nan.

Ya ce gwamnati baza ta sassautawa masu tada kayar baya ba a jihar dama kasa baki daya.

Duk da wannan sanarwa da shugaban kasar yayi, hare-haren ya cigaba da faruwa a fadin kasar a kowacce rana.

Maimakon mayar da hankali wajen kawo karshen wannan lamari, gwamnatin tarayyar ta fara dora laifin kashe-kashen akan wasu mutane.

Idan ba a manta ba, babban mai bawa shugaban kasa shawara a fannin sadarwa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya ne suke taimakawa ‘yan bindigar a jihar Katsina.

KARANTA WANNAN: Sarakunan gargajiya ne suke taimakawa ‘yan bindiga a jihar Katsina – Fadar shugaban kasa

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here