Kungiyar Malamai ta jihar Kano ta kalubalanci Ganduje kan bude Masallatai a jihar

0
168

Kungiyar Malamai ta jihar Kano ta kalubalanci hukuncin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje na bude Masallatai da Coci a jihar.

Sun bayyana cewa bude wuraren bautar ka iya kara yawan yaduwar cutar a cikin al’ummar jihar, ganin yadda ake kara samun masu cutar a jihar a ‘yan kwanakin nan.

Da yake hira da BBC Hausa, kamar yadda Premium Times ta ruwaito, shugaban kungiyar, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce gwamnatin jihar kamata yayi ta fara duba da yadda cutar ke kara yaduwa cikin al’umma kafin ta yanke wannan hukunci.

Ya ce da gwamnati ta nemi shawarar kungiyar Malaman jihar, da ta bukaci a fara la’akari da lafiya al’umma farko.

“A wannan lokaci na annoba tunda gwamnati ta amince da a gabatar da sallah a jam’i, ya kamata mutane suma su san abinda yake yi musu ciwo kada suje su sanya rayuwarsu a halaka, musamman wadanda basu da cikakkiyar lafiya su zauna a gida shi yafi.

“Wadanda suke ganin za su iya zuwa Masallaci, idan har lafiyarsu lau zasu iya zuwa suyi sallah a cikin jam’i.

“Babu laifi akan wanda bai je shi Masallaci ba mutukar yana da kwakkwaran dalili,” cewar Sunusi Khalil.

Idan ba a manta ba a cikin makon nan ne Press Lives ta kawo muku rahoton cewa gwamna Ganduje ya cire dokar hana sallah a cikin jam’i a jihar, inda ya bawa mutane damar gabatar da sallar juma’a da ta idi a jihar, amma da sharadin bin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here