Kudi na inda suke: Za a ci tarar miliyan 20 ko zaman gidan yarin shekara 3 ga duk wanda aka kama babu takunkumin fuska a kasar Qatar

0
146

A jiya Alhamis ne ministan cikin gida na kasar Qatar ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta sanya dokar dole duk wanda zai fita daga gida a kasar ya sanya takunkumin fuska.

Ya bayyana cewa dokar za ta fara aiki daga ranar Lahadin nan, inda ya ce duk wanda ya karya doka za a ci tararshi riyal 200,00 kimanin naira miliyan ashirin kenan a kudin Najeriya.

Haka kuma wanda ba zai iya biyan wannan kudin ba dole ne yayi zaman gidan yari na tsawon shekara uku, kamar yadda sanarwar da aka wallafa a shafin ma’aikatar na Twitter.

A wani taro da suka gabatar ranar Laraba, ‘yan majalisar kasar sun mayar da sanya takunkumi doka a kasar, inda suka ce: “Dole ne mutum ya sanya takunkumi a duk lokacin da zai fita daga gida, koda kuwa shi daya yake tafiya a kafa ko a mota,” cewar kamfanin dillancin labarai na kasar.

Dokar wacce aka sanya ranar Laraba za ta fara aiki ranar Lahadi dinnan, haka kuma za ta cigaba da aiki har lokacin da gwamnati za ta dakatar da dokar.

Kasar Qatar wacce ke da yawan mutane miliyan 2.75, mutum 1,733 sun kamu da cutar coronavirus a kasar a cikin awanni 24 da suka wuce, inda yawan mutanen dake da cutar ya kai mutum 28,272, mutum 14 kuma suka riga mu gidan gaskiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here