Kudi na inda suke, Ahmed Musa ya nuna jerin motocin da ya mallaka a wani sabon bidiyo

0
1011

Fitaccen dan wasan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya zama daya daga cikin ‘yan wasan da suka yi suna sosai a wasan kwallon kafa na duniya da aka buga a shekarun baya.

Dan wasan da yanzu yake a kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr dake kasar Saudiyya ya samu nasarar zura kwallaye a wasan da aka buga na Afrika a shekarar (2014 da 2018).

Haka kuma ya kara yin suna sosai sanadiyyar taimakawa abokanan kungiyarshi wajen ganin suma sun samu nasarar zura kwallo a raga.

Tsohon dan wasan Leicester City dake kasar Ingila ya nuna wurin da yake ajiye motocinsa a lokacin da yake buga wasan Table Tennis tare da wani mutumi da ba a sanshi ba.

Jerin motocin dake wajen ajiye motocin nashi sun hada da Mercedes Benz G-Wagon wacce kudin ta ya kai kimanin miliyan 120, Range Rover Velar wacce ta kai kimanin naira miliyan 40 da kuma Porsche Macan ita ma da kai kimanin naira miliyan 30.

View this post on Instagram

🏓

A post shared by Ahmed Musa MON (@ahmedmusa718) on

Video Source: Ahmed Musa Instagram Page

Ahmed Musa yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka ciwo kofin kwallon kafa da aka buga na Afrika a shekarar 2019 a kasar Egypt.

Dan wasan mai shekaru 27 an bashi mukamin kyaftin din ‘yan wasan Najeriyar bayan tsohon kyaftin din kungiyar ‘yan kwallon Najeriya Mikel Obi ya bar kungiyar.

View this post on Instagram

Alhamdulillah 🙏❤️🥰

A post shared by Ahmed Musa MON (@ahmedmusa718) on

Photo Source: Ahmed Musa Instagram Page

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here