Ku tuba ku ajiye makaman ku ko mu aika ku kiyama – Shugaba Buhari ya gargadi ‘yan bindiga

0
754

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan bindiga akan su tuba su ajiye makamansu ko kuma su fuskanci kisa na wulakanci.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaban kasar ya bayar da wannan gargadi ne a wajen wata ganawa da yayi da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

Shugaban kasar kuma ya yiwa Masari ta’aziyya akan irin rayukan da ake rasawa a jiharsa.

Wasu daga cikin mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar harin da ‘yan bindigar suka kai kwanan nan sun hada da Abu Atiku, Mai Garin ‘Yantumaki dake karamar hukumar Danmusa da kuma shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Batsari, Abdulhamid Sani.

A cewar shugaban kasar, ‘yan bindigar da suka aikata laifi akan mutanen da basu ji ba basu ganei ba, baza su sha a banza ba.

Ya ce za a gabatar da hari akan su a jihohin Zamfara, Sokoto, Niger, Katsina da kuma Kaduna.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai Masari ya bayyana cewa sulhun dake tsakaninsu da ‘yan bindiga a jihar ya zo karshe. Inda ya ce jihar tayi yarjejeniya da ‘yan bindigar amma duk da haka suna kai musu hari.

Masari ya ce ‘yan bindigar sun ci amanar gwamnatinsa, saboda sun bari sai da suka zage dantse suna ta kokarin ganin an cigaba da samun zaman lafiya sai suka dawo da kawo musu hari.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here