Ku sauka a mulki bama yi – Masu zanga-zanga a Katsina sun bukaci Buhari da Masari suyi murabus

0
333

Dubunnan matasa a jiya Talata sun gabatar da zanga-zangar lumana a jihar Katsina, inda suka bukaci shugaba Buhari da gwamna Bello Masari su sauka daga kujerun su.

Zanga-zangar ta biyo bayan hare-haren da ake kaiwa a jihar ana kashe al’umma babu gaira babu dalili.

Matasan wadanda suke zanga-zangar, sun ce gwamnatin tarayya da gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun gaza kare rayukan al’umma daga hannun ‘yan bindigar dake yankin.

Haka a jihar Neja can ma an gabatar da irin wannan zanga-zanga, inda masu zanga-zangar suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki mataki akan matsalar rashin tsaro.

Da yake mayar da martani akan zanga-zangar da ake a jihar ta Katsina, wacce take ita ce mahaifarsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga al’ummar jihar da suyi, inda ya kara da cewa gabatar da zanga-zanga akan tituna da matasa keyi ka iya daukewa jami’an tsaron dake yankin hankali.

Daily Trust ta ruwaito cewa zanga-zangar da aka gabatar jiya ita ce ta hudu a jere da mutanen jihar ta Katsina suka gabatar saboda matsalar tsaron da ake cigaba da samu a jihar.

Anyi zanga-zanga a garin Daddara dake karamar hukumar Jibia, ‘Yantumaki dake karamar hukumar Danmusa da kuma ‘Yankara dake karamar hukumar Faskari.

Zanga-zangar da suka gabatar a jiya, matasan da suka fito daga kananan hukumomi 34 na jihar, sun shirya zagayawa zuwa filin wasa na Kangiwa, dake Kofar Soro da misalin karfe 8 na safe, tare da tinkarar gidan gwamnatin jihar.

Sai dai kuma a lokacin da suke shirin zuwa wadannan wuraren, duka hanyoyin an sanya musu shinge, hakan ya sanya masu zanga-zangar canja hanya.

Matasan sun gabatar da zanga-zangar dauke da alluna da suka yi rubutu kala-kala da suka hada da ‘End the Katsina Killing Now’, ‘Buhari/Masari Resign Now, You Cannot Protect Us’, da dai sauransu

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here