Ku dinga nunawa jama’a ‘yan ta’addar da kuka kashe in dai da gaske ne – Shehu Sani ga gwamnatin tarayya

0
1188

Tsohon Sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya kalubalanci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta dinga fitowa fili tana nunawa ‘yan Najeriya ‘yan ta’addar da take cewa kullum tana kashewa.

Shehu Sani ya bayyana hakane a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 7 ga watan Yunin nan da muke ciki.

Tsohon Sanatan ya bayyana cewa mutane na gani da idonsu a duk lokacin da ‘yan bindigar suka yiwa mutane barna ko kuma suka kashe al’umma, amma kuma ita gwamnati sai dai kawai rubutun iska da take wallafa kullum a shafukan sadarwa babu wata shaida dake nuna cewa lamarin ya faru.

“A duk lokacin da ‘yan ta’adda suka kashe mutane, muna ganin hotuna na abubuwan da suka yi na cin zarafi, yana da kyau duk lokacin da gwamnati ta samu nasara akan ‘yan ta’addar ta dinga sanyawa muna gani irin bajintar da tayi.

Ana ta samun yawaitar kashe-kashen al’umma da ‘yan bindigar suke yi a jihohin Borno,Katsina, Zamfara, Kaduna da sauransu.

A wannan makon ‘yan bindigar sun kai hare-hare da dama a wasu kauyuka dake jihar Maiduguri inda suka kashe mutane da dama suka kone kauyuka.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here