Kowa ya koma gona saboda Najeriya ba ta da kudin da za ta iya siyo kayan abinci daga kasashen waje – Shugaba Buhari

0
557

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Najeriya yanzu bata da kudin da za ta iya sayo kayan abinci daga kasashen waje.

A lokacin da yake hira da manema labarai ranar Idi a gidan gwamnati dake Abuja jiya Lahadi, shugaban ya bayyana cutar coronavirus a matsayin abin tsoro.

Yace annobar ta shafi kasashen da suka cigaba da ma wadanda basu cigaba ba.

“‘Yan Najeriya za su ga cewa yanzu cutar Coronavirus ta shafi duka kasashen da suka cigaba da ma wadanda basu cigaba ba,” ya ce.

“Maganar gaskiya ma mutanen mu basu mutu ba kamar yadda nasu suka mutu. Saboda haka wannan cuta abar tsoro ce.”

Shugaban kasar yayi kira ga manoma da suyi amfani da lokacin damuna wajen noma kayan abinci a fadin Najeriya.

‘Ina fatan mu samu damina mai albarka koda za mu samu isashen kayan abinci,” cewar Buhari.

“Ina fatan manoma za su koma gona koda za mu samu damar noma kayan gona masu yawa ta yadda baza mu damu da siyo kayan abinci daga waje ba.

“Bayan haka ma bamu da kudin da zamu iya siyo kayan abinci daga kasashen waje, saboda haka dole ne mu tashi mu noma abinda zamu ci.”

Ya roki ‘yan Najeriya da su cigaba da bin dokar da hukumomin lafiya suka gindaya akan wannan cuta ta coronavirus.

“Ina shawartar ‘yan Najeriya da suyi takatsantsan suyi amfani da shawarar hukumomin lafiya,” ya ce.

“Ministan lafiya yana kokari sosai wajen wayarwa da jama’a kai dangane da cutar. Saboda haka mu bi a hankali.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here