Kotu ta bada umarnin cafke shugaban karamar hukuma da yayi awon gaba da kayan tallafin talakawa a Kano

0
127

Wata kotun majistire a jihar Kano ta bayar da umarnin kamo shugaban karamar hukumar Kumbotso, Kabiru Ado-Panshekara.

Kotun ta bayar da wannan umarni ne bayan shugaban karamar hukumar yaki bayyana a gabanta ya kare kanshi akan laifin da ake tuhumarsa na cin amana.

Ado Panshekara wanda aka bawa amanar rabawa talakawa kayan tallafi don rage musu radadin zaman gida da aka tilasta su a wannan lokacin, ana zarginshi da bawa mutanen da basu aka ce ya bawa ba.

Lauyan mai gabatar da kara, Salisu Tahir, wanda ya zargi shugaban karamar hukumar da sabawa sashe 315 na dokar shari’a da kuma sashe 26 na dokar yaki da cin hanci da rashawa na shekarar 2008.

Salisu Tahir ya tabbatar da cewa kotun ta bayar da umarnin Kabiru Ado Panshekara ya bayyana a gabanta a ranar 13 ga watan Mayu da misalin karfe 9 na safe.

Lauya mai kare wanda ake kara, Ibrahim Adamu ya bayyanawa kotu cewa ba shi da masaniya akan inda wanda ake zargin yake, inda ya roki kotu ta dakatar da shari’ar na tsawon mintuna 30.

Ya zuwa yanzu dai a daga sauraron karar har zuwa ranar 27 ga watan Mayu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here