Kotu ta bada umarnin biyan naira miliyan 10 ga mutumin da ya kai karar ‘yar gidan shugaban kasa Hanan Buhari

0
242

Wata babbar kotun tarayya dake zaune a Asaba, jihar Delta ta bayar da kyautar naira miliyan goma ga Anthony Okolie, wanda hukumar DSS ta tsare akan yayi amfani da layin wayar da ‘yar gidan shugaba kasa Hanan Buhari tayi amfani da shi.

Idan ba a manta ba a ranar 19 ga watan Yulin shekarar 2019, Anthony, wanda yake dan kasuwa ne a Asaba, ya shiga hannun hukumar DSS, inda suka tsare shi akan yayi amfani da tsohon layin ‘yar gidan shugaban kasa Hanan Buhari bisa rashin sani.

A cewar Anthony, an tsare shi cikin ankwa har zuwa ranar 22 ga watan Satumbar shekarar 2019, tsawon makonni goma kenan, inda hukumar ta DSS ke jiran Hanan wacce ke makaranta a kasar Ingila a lokacin ta dawo gida Najeriya.

Bayan an sake shi, mutumin ya maka hukumar DSS, ‘yar gidan shugaban kasa Hanan da kuma kamfanin MTN a kotu, inda ya bukaci a bashi naira miliyan 500 akan cin zarafinsa da aka yi.

Sai dai a ranar Alhamis kotun wacce mai shari’a Nnamdi Dimg ke jagoranta ta bukaci hukumar DSS ta biya Anthony naira miliyan goma akan cin zarafin shi da tayi, amma tayi watsi da karar akan Hanan Buhari da kuma kamfanin MTN, inda ta ce babu wata shaida akan Hanan din da kuma kamfanin MTN.

Hukumar DSS din ta bayyanawa kotu cewa sun bi umarni ne daga fadar shugaban kasa akan su kama Okolie saboda yayi amfani da tsohon layin ‘yar gidan shugaban kasar wajen damfarar mutane kudi, zargin da lauyoyin Okolie suka karyata kenan.

Wani lauyan Okolie, mai suna Tope Akinyode, ya tabbatar da faruwar lamarin a kotu, bayan ya wallafa labarin a shafinsa na Twitter, inda yace ya samu nasara akan kotun tarayya ta amince za ta saka hukumar DSS ta bayar da naira miliyan goma akan cin zarafin da ta yiwa Anthony.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here