Komawar wata budurwa addinin Kiristanci ya jawo kace nace a yanar gizo

0
444

Wata budurwa mai amfani da shafin sadarwa na twitter, ta bayyana cewa ta koma addinin Kiristanci, sai dai mutane sun dauki abin da zafi sosai, yayin da lamarin ya juye ya zama tamkar rikicin addini.

Duk da dai budurwar bata bayyana ainahin addininta ba, amma wannan abu da ta wallafa ya sanya, Musulmai, Kiristoci da wadanda ma basu da addini suka dinga yin sharhi.

Budurwar mai suna Ema ta rubuta cewa: “Yau na koma addinin Kiristanci,” sannan ta kara da cewa, “Ina fatan za ku girmama hukuncin dana yanke”

Kiristoci sunyi ta yi mata san barka akan hukuncin da ta yanke suka kuma yi mata murna zuwa addininsu. Inda su kuma Musulmai suka nuna rashin jin dadinsu, duk da dai budurwa bata bayyana ko a farko ita Musulma ba ce. Su kuwa wadanda basu da addini, sun bayyana mata cewa yaudararta ake yi da addini.

A yanzu haka dai mutane na ta cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari na budurwar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here